✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta kashe mutum 9 a Najeriya, 917 sun kamu

A ranar Lahadi an samu karin mutum 9 da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus a yayin da aka samu mutum 917 sabbin kamuwa.…

A ranar Lahadi an samu karin mutum 9 da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus a yayin da aka samu mutum 917 sabbin kamuwa.

Hakan na kunshe ne cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa NCDC ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.

Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 222 da suka kamu a Abuja, sai mutum 214 a Jihar Legas da kuma karin mutum 92 a Jihar Filato.

A Jihar Nasarawa an samu mutum 50, sai Oyo mai mutum 41 da kuma  Adamawa mai mutum 33 yayin da aka samu mutum 32 a Ondo.

Cikin sa’a 24 an samu karin mutum mutum 28 a Abiya, da mutum 19 a Ogun sai mutum 17 da suka harbu a Jihar Ribas.

Jihar Kano ta samu karin mutum 16, sai Yobe na da mutum 14 da kuma mutum 8 a Edo, sai Anambra mai mutum 6 yayin da kuma aka samu karin mutum 5 a Ekiti da kuma mutum daya a Jigawa.

A jimillance yanzu cutar Coronavirus ta harbi mutum 90,080 a fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun 2020.

Kazalila, alkaluman na NCDC sun nuna cewa cutar ta kashe adadin mutum 1,311 yayin da tuni an salami mutum 75,044 bayan samun waraka.