Coronavirus ta yi ajalin mutum 27 cikin tsawon kwanaki biyar a fadin Najeriya, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar zuwa 3,058 tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun 2020.
Hakan dai na kunshe cikin sabbin alkaluman da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya NCDC ta fitar a ranar Alhamis.
- Dubban mutane sun halarci jana’izar Dokta Ahmad Bamba
- Pogba zai zama dan wasa mafi albashi a tarihin Firimiya
Bayanan da NCDC dangane da alkaluman cutar, ta bayyana cewa da tun daga ranar 1 zuwa 5 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2022, an samu mutum 3,063 ta cutar Coronavirus ta harba fadin kasar.
A kan haka ne NCDC da kuma Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Najeriya (NPHCDA) suke ci gaba da nanata muhimmancin karbar riga-kafin, la’akari da yadda ake samun sabbin nau’ikan cutar suna kara bayyana a fadin duniya.
A bayan nan ne dai a daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da barazanar samfurin COVID-19 na Omicron mai saurin yaduwa, masana ilimin kimiyya sun sake gano wani sabon samfurin mai suna ‘IHU’.
Binciken dai ya gano sabon samfurin na da nau’o’i har 46, kuma ya zuwa yanzu ya kama mutum 12 a kasar Faransa.
A cewar binciken, an gano mutum na farko da ya kamu da cutar ya yi tafiya a ’yan kwanakin nan zuwa kasar Kamaru, kamar yadda masu binciken suka wallafa a mujallar medRxiv.
To sai dai masana sun yi gargadin cewa ba lallai ne don an gano samfurin ya kasance yana da saurin yaduwa kamar ragowar samfuran ba, ciki kuwa har da na Omicron.