An samu karin mutum takwas da suka rasa rayukansu sakamakon cutar Coronavirus a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da Hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta fitar a yammacin ranar Asabar.
- An tura tawagar bincike ta musamman kan kisan matafiya a Jos
- Girgizar kasa ta kashe mutane 300 a Kasar Haiti
Yanzu jimillar adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya daga zuwa 2,219 tun bayan bullarta karon farko watan Fabrairun bara.
Kazalika, alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna an samu karin mutum 665 sabbin kamuwa da cutar a Jihohi 13 da kuma Abuja cikin awa 24 da suka gabata.
Jihohin da aka sabbin kamuwar sun hada da Legas (369), Anambra (68), Oyo (63), Akwa Ibom (48), Kwara (28), Ribas(26), Edo(21), Ekiti (15), Ondo (13), Delta (7), Abuja (3), Ogun (3), da kuma Gombe (1).
Ya zuwa yanzu, jimillar mutum 181,962 ne suka kamu da cutar da kuma adadin mutum 166,826 da suka warke.