Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC, sun nuna cewa an samu karin mutum 838 da cutar Coronavirus ta harba ranar Lahadi a fadin kasar.
Cikin bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo kamar yadda ta saba duk rana sun nuna an kuma samu karin mutum bakwai da suka mutu sakamakon cutar a fadin Najeriya.
- An hako sabbin rijiyoyin mai a Saudiyya
- COVID-19: Saudiyya ta ba da izinin kwashe ’yan kasashen waje
Sabbin alkaluman da suka nuna an samu karin mutum 838 da suka harbu sun fito ne daga jihohi 16 da suka hada da; Abuja (297), Legas (253), Filato (82), Kaduna (57), Katsina (32), Nasarawa (31) da Kano (25).
Sauran su ne; Gombe (24), Oyo (8), Ribas (8), Zamfara (7), Ogun (4), Bauchi (4), Edo (4), Anambra (1) da kuma Sakkwato (1).
Da wannan adadi, jimillar mutum 84,414 sun harbu da cutar a Najeriya, yayin da kuma mutum 1,254 suka riga mu gidan gaskiya.
Ya zuwa yanzu dai an salami mutum 71,034 daga cibiyoyin killace masu dauke da cutar bayan sun samu waraka.