An samu karin mutum 3 da suka mutu sakamakon cutar Coronavirus a ranar Talata yayin da kuma aka samu karin mutum 749 da suka kamu da cutar a fadin kasar.
Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Najeriya NCDC ce ta wallafa hakan a shafinta na yanar gizo kamar yadda ta saba duk rana.
- Yadda Sarkin Kano ya kaiwa Kwankwaso ziyara kan rasuwar Mahaifinsa
- Kotu ta ba da umarnin yi wa matasa biyu bulala 12 a Kano
Alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna an sabbin kamuwar sun fito ne daga wasu jihohi 19 ciki har da Abuja.
Bayanan sun nuna cewa an samu karin mutum 299 da suka harbu a Jihar Legas, 131 a Filato, Kaduna ta mutum 83, Abuja mutum 74 sai Jihar Kwara mai mutum 35.
Sauran su ne kamar haka, Sakkwato (26), Edo (18), Kano (17), Katsina (16), Delta (11), Nasarawa (10), Ondo (9), Bauchi (9), Ribas (5), Akwa Ibom (3), Jigawa (1), Osun (1) da Ekiti (1).
Kawo yanzu, jimillar mutum 85,560 ne suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairu.
Kazalika, taskar bayanai ta NCDC ta nuna ya zuwa yanzu an samu jimillar mutum 71,937 da suka warke yayin da kuma mutum 1,267 suka riga mu gidan gaskiya.