Mutum 4 ne suka mutu ranar Talata a fadin Najeriya sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus, lamarin da ya kawo jimillar adadinsu zuwa 1,231.
Hakan na kunshe ne cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren jiya na Talata, 22, ga watan Disambar 2020.
Alkaluman na NCDC sun nuna cewa an samu karin sabbin mutum 999 da cutar ta harba a birnin Abuja da wasu jihohi 17 daga cikin 36 da ke fadin kasar.
Sabbin mutane 999 da cutar ta harba daga jihohin 18 sun kasance kamar haka: Abuja (416), Legas (324), Kaduna (68), Plateau (42), Kwara (32), Kano (24), Gombe (14), Sokoto (12) da Yobe (12).
Saura su ne: Akwa Ibom (11), Bayelsa (10), Ribas (7), Bauchi (7), Ogun (6), Oyo (5), Edo (4), Taraba (4) da Jigawa (1).
Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 79,789, sai kuma mutum 68,879 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka.
Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, an yi wa mutum 903,800 gwajin cuttar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun bana.
Kazalika, alkaluman na NCDC sun nuna cewa mutum 9,679 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.