Wani dan Najeriya da aka sallama daga cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus ya bayyana yadda rayuwarsa ta kasance.
Mutumin, wanda ya yi kwana 14 inda ake killace majinyatan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, ya yi bayani ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC.
Ga dai abin da yake cewa:
Abin da ya faru na dawo daga tafiya ranar Juma’a, sai na ce bari na kaurace kamar yadda ma’aikatan lafiya suka tanadar a Najeriya.
[Don haka] bayan na dawo kawai sai na wuce dakin da yake bangaren yaran gida ranar Asabar, sai na kira jami’an Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sai suka zo suka dauki jinina.
Sai washe gari suka kira ni kamar karfe 10:00 na safe, amma sakamakon ya nuna ina dauke cutar Covid -19.
Ina jin hakan sai na ce ‘Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un’, saboda faduwar gaba.
To sai na ce masu yanzu mene ne abin yi? Sai suka ce suna nan zuwa yanzu za su kai ni cibiyar da ake killace mutane masu dauke da irin wannan cutar a Gwagwalada.
Sai na ce Alhamdulillahi.
Sai na yi wa mai dakina bankwana, [na ce mata] kin ji abin da ya faru gara da muka yi wannan tsarin na zama a dakin yaran gida.
Da ma tunda ka dawo daga tafiya baka zauna a cikin iyalanka ba?
Ban zauna ba gaskiya.
Da aka kai ka can Gwagwalada yaya yanayin wurin yake, yaya ka dinga ji?
A gaskiya ranar farko da tunanunka iri-iri na dan-Adam na dinga yi, tun da kullum kana gani a waya kana gani a talabijin da sauran kafofin sada zumunta cewa cutar tana kisa, tsoro ya shiga haka, amma bayan kwana biyu da yake likitocin kwararru ne suka yi mana bayani suka ce cutar nan ba wai kabari salamu alaikum ba ne, cutar nan ana warkewa, an ma fi warkewa.
Sai hankalina ya fara kwanciya.
Yadda na ga wurin kuma gaskiya a gwamnatance, ya kamata a yi wa gwamnati godiya a yaba masu.
Maganar gaskiya ita ce asibiti ba gida ba ne bai yiwuwa a ce duk abin da ke gida ka same shi a asibiti, amma a takaice sun yi kokari.
Wato kowane mara lafiya da dakinsa.
Kullum ake zuwa a yi maku allurai a ba ku magani ko ana zabar kwanakin da ake yi maku haka?
A’a, ranar da ka zo za a ba ka magunguna, irin wadanda suka ga ya dace da yanayinka.
Saboda su likitocin sun ce akwai wadanda suke zuwa da ciwo mai tsanani, akwai wadanda suke zuwa da tsaka-tsakiya, akwai ma wanda bai da wata alama yana dauke da wata alamar cutar.
Ni yau na yi kwanaki 14 a killace, har yanzu ba ni da wata alama ta rashin lafiya.
Bisa hakan ne ranar Litinin aka yi min gwaji, sakamakon ya nuna ba na dauke da cutar.
Sai da na ce wa likitar “kin duba sosai kar na soma murna fa?” Ta ce ta duba, wannan sakamakon na biyun ke nan da ya nuna ba na dauke da cutar kuma na yi wa Allah godiya sosai, na ce Ubangiji Allah Ya tsare gaba.