Ma’aikatan lafiya na cibiyar kula da marasa lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Idi Aba (FMC), a Abeokuta a jihar Ogun sun shiga rudu bayan da wata mace mai ciki ta mutu a cibiyar.
An kwantar da mai cikin ne a cibiyar ta FMC Abeokuta, daga bisani kuma aka dauki sanfurin gwajin cutar a jikin ta da kuma na wata mace da karin wani mutum guda.
Matar mai cikin ta rasu tun kafin sakamakon gwajin ya fito, bayan rasuwar ta ne gwajin ya nuna tana dauke da cutar, da kuma dayan mutumin da aka dauki samfurin gwajin su tare, sai dai dayar matar gwajin ya nuna bata dauke da cutar.
Sakamakon gwajin ne ya sanya ma’aikatan cibiyar lafiyar ta Gwamnatin Tarayya ta Abeokuta suka shiga zullumi kasancewar an kwantar da mai cikin a cibiyar inda akalla likitoci hudu suka duba lafiyar ta, kana an sauya mata dakin kula da ita a ƙalla sau hudu tun daga lokacin da aka kai ta cibiyar.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a kai ga killace jami’an lafiyar da su kayi ta’ammali da matar ba.
Wakilin Aminiya ya tuntubi mai magana da yawun cibiyar ta FMC Abeokuta, Mista Segun Orisajo wanda ya shaida cewa ba zuwa yanzu ba shi da hurumin cewa wani abu akan maganar, ” ba zan iya magana yanzu ba akan wannan lamari, amma ka bani lokaci bayan mun tattara bayanai da manyan jami’an cibiyar damasu ruwa da tsaki a harkar lafiyar jihar Ogun, Zan yi maka karin haske”
A na ta bangaren kwamishiniyar kiwon lafiya ta jihar Ogun Dakta Tomi Coker, ta shaida cewa ta sami labarin mutuwar mai juna biyun amma bata kai ga samun bayanai kan musabbabin mutuwar ta ba, zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Tuni dai aka killace dayan mutumin da aka tabbatar ya kamu, a cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Ikenne, yayin da gawar matar ke dakin ajiyar gawa na FMC Abeokuta.