✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Mutum 13 sun warke, 5 sun mutu a Edo

An sallami mutum 13 da suka warke daga cutar coronavirus a Jihar Edo inda cutar ta yi ajalin karin mutum biyar. Gwamna Godwin Obaseki ya…

An sallami mutum 13 da suka warke daga cutar coronavirus a Jihar Edo inda cutar ta yi ajalin karin mutum biyar.

Gwamna Godwin Obaseki ya sanar da haka ta shafinsa na Twitter a yan Litinin.

“Karin mutum 5 sun rasu, yanzu mutum 24 cutar ta kashe. An kuma sallami mutum 13 da suka warke”, a cewarsa.

Ya ce, “Daya daga cikin mamatan ya rasu ne a Asibitin Stella Obasanjo, sauran 4 kuma a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin”.

Da yake bayar da alkaluman cutar a jiharsa Obaseki ya ce, “…galibin wadanda cutar ta kashe ‘yan shekara 60 zuwa sama.

Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su rika bin shawarwari da dokokin kariya daga yaduwar cutar.

%d bloggers like this: