Tun bayan rufe makarantun Boko da na Islamiya da gwamnatocin tarayya da na jihohi suka yi a watan Maris na bana da nufin dakile yaduwar cutar coronabirus, mafi yawan malaman makarantu, musamman masu zaman kansu sun tsinci kansu cikin matsananciyar rayuwa.
Akasarinsu sun kwashe watanni babu albashi, sannan ga shi suna da iyalai da suke dogaro da su.
Sannan babu wani tallafi da suka samu na musamman daga Gwamnatin Tarayya ko na jihohinsu.
Su kansu masu makarantun sun dogara ne da kudaden da iyayen yara ke biya wajen daukar nauyin iyalansu da kuma biyan albashin malamai da ke koyarwa a makarantun nasu.
Aminiya ta samu zantawa da wasu daga cikin malaman boko da na Islamiya, inda suka bayyana cewa har yanzu suna cikin wani yanayi domin fa suna wahala matuka.
Mun zama mabarata –Malamai
Wani malami da ke karantarwa a wata makaranta mai zaman kanta a yankin Gwarimpa Abuja, Malam Nasiruddin Abdul-Ganiyu ya ce suna shan wahala a halin yanzu, inda suka dogara daga tallafin sadaka da wasu daidaikun jama’a ke ba su.
Ya ce a farkon lamarin wasu daga cikinsu sun koma yin aikin acaba.
“Sai dai abin takaici shi din ma gwamnati ta zo ta hana a nan Kubwa, inda nake da zama da mata biyu da nake aure da kuma ’ya’ya 9.
“Motata ta shiga da zan iya bin hanya da ita don neman na abinci, ta samu matsala kuma babu abin da zan iya gyranta da shi.
“Akwai wasu ’yan uwa biyu da na sani da suke aikin koyarwa, yaya da kani, sun kukuta sun samu keke, daya zai yi aiki daga wayewar gari zuwa karfe 2 na rana, sai dayan kuma ya karba daga lokacin zuwa aikin dare.
“Mun dauka a lokacin da gwamnati ta yi maganar ba da tallafin coronavirus za ta bai wa makarantu masu zaman kansu muhimmanci, ganin dama wadanda ke karkashinta na samun albashinsu.
“Amma har yanzu ba mu gani ba, sai muka ji ana cewa kada dalibai su biya kudin makaranta na zango na uku.
“Wannan ba aldaci ba ne. Muna fatan Allah zai shiga zukatan shugabanninmu na gwamnati su yi abin da ya dace saboda basussuka da muka ci a sanadin wannar dokar sun yi mana dabaibayi a wuya.
“Matsalar ta hada da malaman makarantun Islamiyya a yankin na Abuja, wadanda hukumominsu su ma ke bin umarnin dokar”, inji shi.
Malam Abubakar Abdurrahman malami ne a wata makarantar kudi a Katsina.
Ya ce, “A farkon watan da aka rufe makarantun har zuwa wata na biyu, an biya rabin albashi amma yanzu gaskiya sai a hanakali, domin shugabannin makarantar sun ce babu kudi saboda iyayen yara ba su biya ba”, inji shi.
Shi kuwa wani malamin da ya nemi a sakaya sunansa, cewa ya yi har zuwa yau makarantar da yake koyarwa ba a ba shi ko sisi ba da sunan albashi.
Malamin ya kara da cewa, da ma rashin aikin yi ne ke sanya su shiga irin wadancan makarantu masu zaman kansu.
A yanzu har ta kai bashin da yake ci ya bari, gudun kada ya shiga cikin wani hali.
Ba dalilin biyan kudi
Shi kuwa wani mahaifin wasu dalibai da ke makarantar kudi, wanda bai so a ambata sunansa, cewa ya yi babu dalilin da zai sa ya dauki kudinsa ya kai makaranta ba tare da an koyar da yaronsa ba.
“Ai tamkar aikin leburanci ne, in ka yi mani aiki in biya ka, to babu aikin kudin me zan biya?”
Aminiya ta samu labarin cewa akwai wadanda ke daukar malaman da ke zuwa gida suna koyar da yaran suna biyansu.
Malam Muntari cewa ya yi, “tun da lalura ce ta kawo rufewar wadannan makarantu ba don son ransu ba, ya kamata a ce iyaye su rika biyan koda rabi ne na kudaden da suke biya, domin ganin cewa ana ba malaman wani abu, tun da akwai ranar da za a bude makarantun a ci gaba da aiki.
Ya ce amma kin biyan zai sa malaman su rika kallon iyayen da wani abu na rashin tausayi, wanda hakan ke iya sa makarantun daukar wasu matakan da kuma iyaye za su yi kuka da su na rashin kyautatawa.
Malam Salisu Ibrahim malamin boko ne a wata makaranta a Tudun Nufawa Kaduna.
Ya ce hakika tun watan Afrilu rabonsa da karbar albashi.
“A wannan watan ne aka ba malamai rabin albashin watan Afrilu, tun nan ba a sake samun kudi ba.
“Kai dai a bar zancen kawai amma dai malamai na boko da Islamiya masu zaman kansu na cikin wani yanayi mara dadi.
“Wasu lokutan sai dai ka ga malami ya kira abokin aikinsa yana neman bashin Naira dubu daya ko biyu da zai saya wa yaransa abinci a gida.
“Kuma ga shi gwamnati ta mance da mu, ko tallafi ba a ba malaman makaranta masu zaman kansu ba”, inji shi.
Game da yadda yake rayuwa, sai ya ce kaji da yake kiwo tun kafin zuwan cutar coronavirus ya rika sayarawa domin biyan bukatunsa da na iyalali.
Sake bude makarantu
Game da yadda suke ji dangane da matakin gwamnati na bude makarantu sai ya ce “gaskiya abin bai yi mana dadi ba, duk kuwa da mun san cewa ko da an koma a yanzu ba wani kudi za a samu ba amma akwai dadi a ce kullum kana fita iyalinka su ce da kai a dawo lafiya.
“Domin a yanzu a kullum muna zaune ne babu abin da muke yi, sannan abokanmu da ke wasu ayyuka suna fita kullum amma kai malamin makaranta kana gida kuma ga shi ba wai kana sa ran samun wasu kudi ba ne a karshen wata.
“Babu wanda ya san yadda kake rayuwa da iyalinka ko yadda kake ciyar da su. Allah dai Ya taimake mu kawai”, inji malamin.
Aminiya ta zanta da wasu malaman makarantu masu zaman kansu a Legas, inda suka shaida mata cewa cutar coronavirus ta mayar da su tamkar mabarata saboda rashin aikin yi da kuma rasa hanyoyin kudin shiga.
Malama Halima Mu’azu tana karantarwa ne a makarantar boko a Unguwar Hayin Malam Bello, Rigasa Kaduna, sannan tana aiki a wata Islamiya da ke titin Matazu a Sabon Garin Kaduna.
Ta ce “gaskiya rayuwar dai da sauki saboda ni matar aure ce kuma mijina na aikinsa saboda haka yana daukar nauyinmu, amma idan na dubi sauran mazan aure da ke karantarwa sai in rika tausayinsu.
“Domin akwai wacce na sani, ita da mijinta duk karantarwa suke yi a makarantar boko amma a yanzu haka abin a tausaya musu ne tun da ba a zuwa makaranta kuma ba wani aiki suke yi ba sai karantarwar”, inji ta.
‘Ba ma iya biyan albashi’
Abdulganiyu Abdulrahman Giwa, shi ne mai Makarantar Ikra Standard Academy da ke Titin Musawa a Zango, Tudun Wada Kaduna.
Ya bayyana cewa tun bayan rufe makarantun da aka yi babu wani malami da ya biya albashi domin babu kudin biyan su.
“Ban san wani tallafi ba da ake bayarwa tun da ni ban samu ba ni ma. Ni kaina ina bukatar tallafi a yanzu”, inji shi.
Game da ci gaba da rufe makarantun, ya ce “Idan har da gaske gwamnatin take cewa yin hakan shi ne zai kare rayuwar yaran da mu, babu damuwa.
“Duk da dai duk abin babu dadi a ce ka saba zuwa aiki amma a yau a ce ba ka aiki”, inji shi.
Hukumar gudanarwa ta Makarantar Gidauniyar Ilmantarwa a Tsarin Musulunci da ke Kubwa Abuja da a ka fi sani da suna Model Islamic Educational Fundation, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta cika alkawari da ta dauka na tallafa wa makarantu masu zaman kansu a sakamakon annobar coronavirus da ta tilasta rufe makarantu baki daya.
Daya daga cikin ’yan kwamitin amintattu na makarantar, Malam Idris Isma’ila ne ya bayyana bukatar a yayin zantawa da Aminiya.
Malam Idris Isma’il ya ce makarantar ta samu kanta cikin halin ni-’yasu tun lokacin da aka rufe daukacin makarantu.
Ya ce makarantar tana tafiyar da wata gidauniya ta musamman da ke gudanar da ayyukan jinkai da suka hada da tallafa wa mabukata da samar da wuraren alwala da gyaran bahaya a masallatai da kuma makarantun boko da na Islamiyya a yankunan da ke da kusanci da ita, baya ga biyan albashin ma’aikatanta a kan kari da ya ce take yi.
“Duk wannan ya tsaya yanzu. A watan farko biyo bayan umarnin dokar, mun biya ma’aikata albashinsu dari bisa dari, sai wata da ya biyo baya, aka biya rabi a wata na uku kashi 25 a cikin 100 na albashi ne aka biya.
“To ga shi wannan watan da ya kare ba mu iya biyan su ko kwabo ba”.
Ya ce sun ji labari ta kafofin yada labarai kan gwamnati za ta ba da tallafi na musamman ga makarantu.
“Idan gwamnati ta yi la’akari da gudunmawa da makarantun nan ke bayarwa wajen magance aikata laifuffuka ta hanyar ba da tarbiyya ga yara da kuma samar da aikin yi, ai mun cancanci ta tallafa wa.
A Jihar Legas, Owokogun Zubair da ke mallakar makarantar Citadella ta koka duba da halin da masu makarantun suka samu kansu.
Ta ce annobar coronavirus ta haifar da matsalar da ba ta kyale kowa ba.
“Muna cikin matsala kwarai, tun ranar 20 ga watan Maris gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantu a fadin kasar nan.
“Ni a nawa bangaren, na iya biyan ma’aikatana albashin watan Afrilu, tun daga nan ban iya biya ba, domin makarantunmu sun kasance a rufe.
“Iyayen yara ba su biyan kudin makaranta amma dole ne mu biya masu gidajen da muke haya kudi duk da makarantun namu sun kasance a rufe.
“Malaman makarantunmu sun shiga wani hali, babu wani tallafi da suka samu kuma hanya daya da za a tallafa musu shi ne a bude makarantu su ci gaba da aiki.
“Mu abin da ya fi damun mu shi ne koma bayan da wannnan matsala ta haifar a karatun ’ya’yanmu.
“Kamata ya yi a bude makarantun nan cikin tsarin bin matakan kariya, da suka hada da tsafta, ba da tazara da auna yanayin zafin jikin mutum.
“Makarantu masu zaman kansu a shirye suke su cika wannan ka’idojin,” inji ta.
‘Muna tsammanin tallafi’
Shugaban kungiyar Masu Makarantun Kudi ta kasa, Mista Yomi Odubela ya bayyana cewa masu makarantun kudi da ma’aikatansu sun kusa darawa.
Ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da jaridar Punch, inda ya ce “mambobinmu sun kusa darawa.
“Kwanakin baya Majalisar Zartarwa ta amince da wasikarmu, inda muke bukatar a tallafa mana domin mu samu biyan malamanmu albashi.
“Sannan mun bukaci a agaza mana da abubuwa da za mu yi amfani da su wajen kare yaduwar annobar a makarantunmu.
“Don haka ina yi wa mambobinmu albishir cewa sun kusa darawa kuma ya kamata duk makarantar kudi ta zama mamba a kungiyar”, a cewarsa.
“Akwai rahotannin cewa wasu masu makarantun sun mayar da makarantun ko dai wajen kiwon kaji ko wani abun daban.
“Sannan kuma wasu malaman sun dauki alwashin neman wani aikin, don haka ba za su dawo ba ko an bude makarantun.