Abubakar Danjuma Maiwada matashi ne da ke aiki a Cibiyar Binciken Makamashi ta Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma ya shahara wajen kirkirar kayan amfanin yau da kullum.
A baya-bayan nan ya kirkiri na’urar wanke hannu ta musamman domin kare yaduwar annobar coronavirus.
A hirarsa da Aminiya ya yi bayanin yadda na’urar ke aiki da kuma dalilinsa kirkirar ta a wannan lokaci na annobar coronavirus.
Waye Abubakar Maiwada?
Sunana Injiniya Abubakar Danjuma Maiwada, ina aiki ne da Cibiyar Binciken Makamashi (renewable energy) a Jami’ar Bayero da ke Kano. Ni mutum ne da ke da sha’awar kere-kere.
Abaya na kera kayayyakin amfani na yau da gobe da suka hadar da injin kyankyasar kwan kaji mai amfani da hasken rana, da keke wato laulawa mai amfani da hasken rana, da na’urar samar da iskar gas daga kashin shanu da dai sauran kayayyakin da na kirkira.
Kuma yanzu a wannan lokaci na annobar COVID-19 sai na kirkiri na’urar wanke hannu ta musamman domin ni ma na ba da tawa gudunmawar wajen hana yaduwar cutar.
Yadda na’urar wanke hannun ke aiki
Na’urar na aiki ne ta yadda da kazo inda aka girke ta za ka yi amfani da kafa, babu bukatar ka taba kan fanfo da hannunka ko kuma mazubin sabulu ko sinadarin wanke hannu.
Kana zuwa wajen za ka sanya kafa sai ka danna na’urar da aka sanya ta daga kasa da kafar ka, sai ka tara hannunka, sabulu ko sinadarin wanke hannu ya fito.
Daga nan sai ka kuma danna daya na’urar da kafa nan ma sai ruwa ya zubo ka tara hannunka ka wanke.
Ka ga haka ba ka bukatar taba kan fanfo ko mazubin sinadarin wanke hannun da hannunka.
Idan za ka taba da hannunka, wani ma ya zo ya taba, wani ma haka, ka ga an yi ba a yi ba ke nan, ko kuma nace ana yin tufka da warwara ke nan.
Dalilin kirkirar na’urar
Hakika na kirkiri wannan na’ura ne domin ni ma na ba da tawa gudunmawar domin dakile yaduwar wannan annoba, kasancewar masana sun bayyana cewa ana iya daukar ta, ta wajen taba abu da hannu.
To idan aka ce wannan abu ne da wani zai zo ya taba da hannunsa, wani ma ya zo ya taba to ko ta nan ma za a iya dauka.
Don haka na yi nazari na kirkiro abun da za a iya wanke hannu da shi ba tare da an taba shi da hannu ba.
Ko ya al’umma za ta amfana da wannan fasaha?
Akwai hanyoyi da dama da za a iya amfana.
Mahukunta da masu niyyar taimakawa za su iya tuntuba ta domin mun samar da wannan na’ura da dama ta yadda za ta wadata, a rarraba ta, musamman a wajen hada-hadar jama’a kamar masallatai da coci-coci da ofisoshin gwamnati, da bankuna ko kasuwanni, tashoshin motoci da na jiragen sama, da sauran wuraren mu’amala na jama’a da makarantu da makamantansu;
Mussamman a wannan lokaci da ake yunkurin bude wuraren hadahadar jama’a a daidai lokacin da masana ke tsokaci cewa ba ma kai lokacin da annobar za ta bazu sosai a kasar nan ba, wato maganar annobar yanzu aka fara ta a kasar nan.
Don haka in muka sami tallafi zamu iya kikirar na’urar a wadace domin amfanin jama’a.