✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Masallatai da yawa ba su yi Sallar Juma’a ba a Legas

A yau Juma’a masallatai da dama sun kasance a kulle domin bin dokar da gwamnatin jihar Legas ta kafa ta dakatar da duk wani taron…

A yau Juma’a masallatai da dama sun kasance a kulle domin bin dokar da gwamnatin jihar Legas ta kafa ta dakatar da duk wani taron ibada da zai tara mutum sama da 50.

Masallatan Juma’a da dama dai a jihar sun kasance a rufe.

Aminiya ta kewaya unguwannin Agege da Idiaraba a cikin garin Legas inda galibin masallatan Juma’ar yankin suka kasance a rufe.

Sai dai masallatan kungiyar Izala bangaren Jos ba su bi umarnin gwamnatin ta jihar Legas ba, inda suka gudanar da Sallar Juma’a kamar yadda suka saba bisa dalilin cewa hukumomin ba su sanar da su a hukumance ba.