Likitocin da ake sa ran zuwan su Najeriya daga China don su tallafa a yakin da ake yi da cutar coronavirus sun iso.
Rahotanni sun ce jirgin da ya kawo likitocin ya sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da kusan karfe 4.30 na yamma ranar Laraba bayan tafiyar sa’o’i 15 ba kakkautawa daga Beijing, babban birnin China.
Likitocin 15 sun hada da kwararru a fannin cututtuka masu yaduwa, da na cututtukan da suka shafi numfashi, da likitocin kwakwalwa, da na zuciya, da sauran su.
Kungiyar Likitoci ta Najeriya da wasu kungiyoyin kwadago dai sun yi kira da kada a kawo wadannan likitoci ’yan China, amma gwamnatin tarayya ta ce babu gudu ba ja da baya.
Masu adawa da kawo kwararrun na ganin ita kanta kasar ta China ba ta gama samun kanta ba ma balle ta taimaki wani.
Suna kuma nuna fargaba cewa shigowar masanan ka iya zama kitso da kwarkwata.
Sai dai ana sa ran likitocin za su yi mako biyu a killace kafin su fara aiki a kasar.
Likitocin dai na rakiya ne ga wasu magunguna da kayan aiki da suka hada da tan 16 na kayan gwaji, da na’urorin numfashi, da injinan feshin maganin kashe kwayoyin cuta, da amawalin ma’aikatan lafiya, da safar hannu ta roba, da rigunan kare-kai, da tabarau, da na’urorin auna zafin jiki, da sauran kayan aiki.