✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Kano ce ta biyu a yawan wadanda suka kamu a Najeriya

Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar a ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, sun nuna cewa jihar Kano…

Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar a ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, sun nuna cewa jihar Kano ce ta biyu a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya.

Kano ta kere Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja da a baya ke biye da Legas bayan da jihar ta sami karin mutum 80 da suka kamu da cutar ranar Alhamis.

Zuwa yanzu kididdigar Hukumar ta NCDC ta nuna cewa mutum 219 ne suka kamu da cutar coronavirus a jihar Kano.

Alkaluman sun nuna cewa jihar  ce  ke da mafi yawan wadanda suka kamu da cutar a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu inda ta zamo ta biyu kuma take biye  da jihar Legas.

A baya dai Aminiya ta ba da rahotannin yawan mace mace da ake samu a jihar da ma karuwar samun wadanda ke kamuwa da coronovirus lamarin da yasanya gwamnatin tarayya daukar matakai na musamman a jihar.