Gwamnatin Jigawa ta karbi almajirai 524 ’yan asalin jihar wadanda takwararta ta jihar Kano ta mayar gida.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, wanda ya karbi almajiran, ya ce duk da gwamnatin Kano ta duba su, Jigawa ma za ta sake duba almajiran a tabbatar ba sa dauke da wata larura kafin a mayar da su kauyukan da suka fito.
“Sai kwararrun likitoci sun duba su sosai, kuma duk wanda aka samu da wata alama ta coronavirus za a killace shi”, inji gwamnan na Jigawa.
Ya kuma ce yayin mayar da yaran ga iyayensu za a hada su da kudin abinci ko kayan abinci.
- Coronavirus: ‘Abin da ya sa Jigawa ke kula da wadanda suka kamu’
- Dokar hana fita: Yadda rayuwar wasu ta kuntata a Jigawa
Tun da farko da yake mika almajiran, Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Muhammad Sunusi Sa’id, ya ce sun riga sun tantance almajiran sun tabbatar ba sa dauke da wata cuta.
Ya kuma ce jihar Kano ta yanke shawarar mayar da almajiran jihohinsu na asali ne saboda barazanar annobar coronavirus.
“Na dawo da wadannan almajirai ne bisa umarnin mai girma Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje”, inji kwamishinan, wanda ya kara da cewa jihohin Kano da Jigawa ’yan uwan juna ne, akwai alaka mai kyau kuma ana ganin mutuncin juna.
Da yake amsa tambayar manema labarai a kan ko shi ma zai mayar da almajiran da ke Jigawa jihohinsu na asali, Gwamna Badaru ya ce ko zai yi hakan ba yanzu ba, sai bayan wannan annoba ta wuce.
“Yanzu ba daidai ba ne a kori almajirai ana cikin wannan hali”, inji shi.
Wadannan yara dai na cikin almajiran da gwamnatin Kano ta sha alwashin mayarwa jihohi ko kasashensu na asali da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.
Galibin almajirai dai sun fito daga yankin Birnin Kudu.