✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Italiya ta dakatar da harkokin kasuwanci

Hukumomi a Italiya sun ce wajibi ne a rufe dukkan harkokin kasuwancin da ba su zama dole ba har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu.…

Hukumomi a Italiya sun ce wajibi ne a rufe dukkan harkokin kasuwancin da ba su zama dole ba har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Firayi Minista Giuseppe Conte ne ya bayar da umarnin a ci gaba da laluben da hukumomin kasar ke yi don zakulo hanyoyin kawo karshen cutar Coronavirus.

Yawan wadanda suka rasa rayukansu a kasar ta Italiya sakamakon kamuwa da cutar ya yi tashin gwauron zabi da mutum 800 ranar Asabar, lamarin da ya sa adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 5,000.

“Wannan ne bala’i mafi muni da muka fuskanta tun bayan Yakin Duniya na Biyu”, inji Mista Conte, wanda ya kara da cewa, “ayyukan da ke da matukar muhimmanci wajen samar da ababen da al’ummar kasa ke bukata kadai za a kyale”.

Ya kara da cewa za a kyale manyan shagunan sayar da kaya, da shagunan sayar da magani, da gidajen waya, da kuma bankuna su ci gaba da budewa, sannan za a tabbatar da muhimman ayyuka kamar harkokin sufuri su ci gaba da gudana.

A ranar Lahadi ake sa ran gwamnatin kasa ta Italiya za ta zartar da wata doka ta kar-ta-kwana domin aiwatar da wannan kudurin.