Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin dakatar da tarukan ibada a dukkan masallatan Juma’ar jihar da nufin hana cutar Coronavirus yaduwa.
Hakan dai na nufin da wannan umarni na gwamnati ba za a gudanar da sallar Juma’a ba a fadin jihar.
Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane.
A cewarsa, wajibi ne gwamnati ta yi aiki kafada da kafada da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an yi dukkan mai yiwuwa an hana cutar ta COVID-19 shiga jihar balle ta samu wurin zama.
- Musulmin Kaduna sun yi biris da shawarar El-Rufai
- Coronavirus: Gwamnati na bibiyar mutum sama da 4,000
Tun a makon jiya ne dai hukumomi a Najeriyar suka fara kira ko bayar da umarni ga al’ummominsu da su hakura da tarukan addini a masallatan Juma’a da majami’u don hana cutar yaduwa.