Gwamnatin Kaduna ta yi barazanar ayyana dokar hana fita na sa’o’i 24 in har al’ummar jihar suka ki bin umarnin da ta bayar na takaita tarukan jama’a.
Gwamna Nasir El-Rufai ne ya fadi hakan a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar ta kafofin yada labarai, yana nuna takaici da yadda aka ki daukar shawarar da gwamnatin ta bayar a karshen makon jiya cewa a jingine wasu taruka na ibada.
“Gwamnati ba za ta bata lokaci ba wajen ayyana dokar hana fita a fadin jihar idan yin hakan ne hanya daya tilo da za a bi don tabbatar da aiki [da umarnin da aka bayar na takaita wasu abubuwa] da kuma fahimtar da mutane hadarin da muke fuskanta gaba daya”, inji Gwamna El-Rufai.
Gwamnan dai ya ce ganin yadda aka yi biris da shawarar da hukumomi suka bayar a karshen mako, gwamnati ta yanke shawarar daukar matakin tilasta bin shawarwarin.
“Gwamnati ta yanke shawarar matsawa daga matakin bayar da shawara zuwa na tilasta aiwatar da takaita tarukan dimbin jama’a, musamman a masallatai da majami’u”, inji shi.
A karshe makon dai masallatan Juma’a da majami’u da dama ne suka yi biris da shawarar da gwamnatin ta ba su cewa su hakura da tarukan ibada.
Sai dai gwamnatin ta jihar Kaduna ta jaddada bukatar mutane su takaita kai-kawo sai in fita ta zama dole.
Don haka ne, inji El-Rifai, “Gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci ma’aikata daga matakin albshi na 12 zuwa kasa da su zauna a gida har tsawon kwana 30 daga ranar Talata 24 ga watan Maris.
“Ma’aikatan da ayyukansu suka zama dole, misali abin da ya shafi kiwon lafiya, da tsaro, da agajin gaggawa, an dauke masu wannan hanin”.
- Coronavirus: Zaman zulumi a Bauchi, gwamna ya killace kansa
- Coronavirus: Hukumar jiragen kasa ta lashe amanta
Bugu da kari, Gwamna El-Rufai ya ce ’yan kasuwar da ke sayar da magunguna da abinci ne kadai za a kyale su bude shaguna ko rumfunan su na kasuwa.
“Hukumomin tsaro, da ma Hukumar Kula da Kasuwanni ta Jihar Kaduna (wadda za ta yi feshin magani a kasuwannin) za su tabbatar da aiki da wannan umarni ka’in da na’in”.
Gwamnan ya kuma ce zai nemi hukumomin tarayya da su dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Idan ba a manta ba a karshen mako Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen fasinja, amma daga bisani ta jingine dakatarwar, “bayan ta yi nazari a kan lamarin”.
Tuni hukumomi a matakai daban-daban suka ba da umarnin rufe makarantu da wasu wuraren taruwar jama’a a fadin Najeriya.