✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: El-Rufa’i ya karyata rahoton kai shi Legas

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya karyata labaran da ake yada wa a kafar sada zumunta cewa, an kai shi Legas kuma yana cibiyar…

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya karyata labaran da ake yada wa a kafar sada zumunta cewa, an kai shi Legas kuma yana cibiyar kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus ta Legas.
A sanarwar da gwamnan ya fitar da yammacin ranar Litinin a shafinsa na sada zumunta, ya shaida cewa labarin da ake yadawa cewa yana Legas ana kula da shi a can ba gaskiya bane.
” A yau na fita daga inda nake a killace na tsawon sa’a biyu inda na halarci taro ta manhajar bidiyo na  kwamitin karta kwana na Covid-19 na jihar Kaduna wanda mataimakiyar gwamnan Dakta Hadiza Balarabe ta jagoranta, tunda akwai labaran karya da ake yadawa cewa ina cibiyar kula da masu coronavirus a Legas, za mu yi amfani kyawawan hotuna mu karyata labaran karyar.”
Ya ce, babu tantama yau sama da kwanaki 24 kenan yana killace a wani sashe na gidan gwamnatin jihar Kaduna, inda jami’an kiwon lafiya na jihar ke kulawa da lafiyarsa tun lokacin da ya kamu da coronavirus.
” Kamar yadda hoto ya nuna tun daga wannan lokacin ban yi gyaran fuska ba, nayi haka ne domin na dinga tuna wannan lokaci na annobar Covid-19 bayan annobar ta kau, kuma da yardar Allah zamu ga wannan lokacin.”
Gwamnan El-Rufai, ya mika godiyarsa ga daukacin ma’aikatan jihar tare da duk wadanda suke cikin da halin da yake ciki, ya ce yana cikin yanayi mai kyau, ” Kuma ina murmure wa a kwana a tashi, Na gode wa Allah” in ji Malam Nasiru El-Rufa’i.
A ranar 28 ga watan Maris 2020 ne gwamnan El-Rufa’i ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa yana dauke da cutar coronavirus inda ya zamo mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a jihar Kaduna.
Lokacin da El-Rufai ke tattaunawa ta kafar manhajar bidiyo da kwamitin COVID -19 na jihar Kaduna