✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya yau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya da misalin karfe 7:00 na daren yau Lahadi. Sanarwar na bayyana cewa, Shugaban zai yi…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya da misalin karfe 7:00 na daren yau Lahadi.

Sanarwar na bayyana cewa, Shugaban zai yi bayanin ne game da bullar cutar coronavirus a Najeriya wadda ta zama annoba a duk duniya.

Babban Mashawarcin shugaban kan watsa labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa shugaban zai yi jawabin ne ta gidajen talabijin da rediyo na NTA da kuma FRCN, kuma ana sa ran sauran gidajen talabijin da rediyo za su yada jawabin shugaban kai-tsaye.