Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana nan garau cikin koshin lafiya duk da cewa wasu mukarrabansa sun kamu da cutar Coronavirus.
Adesina ya bayyana hakan ne a yayin amsa tambayoyi a cikin shirin Siyasa A Yau na gidan talabijin na Channels.
Duk wannan dai na zuwa ne bayan da kwanakin kadan aka samu labarin yadda annobar cutar ta yi wa Fadar Gwamnatin Najeriya dirar mikiya, inda ta harbi wasu daga cikin hadiman Shugaba Buhari ciki har da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.
Sai dai Adesina ya ce hadiman shugaban kasar da suka kebance kansu bayan gwajin da ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar COVID-19, hakan ya tabbatar da cewa su ma kamar sauran al’umma, mutane ne masu jini a jiki.
Haka kuma Adesina ya ce hadiman shugaban kasar da suka kamu da cutar ba su da kariya ta daban da sauran mutane ga abubuwan da ke faruwa a kusa da su walau na lafiya ko wani abun na daban.
Kazalika, hadimin shugaban kasar ya ce ya yi imani da ubangijinsa ko da ya kamu da cutar sakamakon mu’amala da abokan aikinsa zai warke kamar yadda wadanda suka kamu a baya suka warke.
A game da maganar adadin hadiman shugaba Buhari da suka kamu da cutar ta Coronavirus a baya-bayan nan, Adesina ya ce wannan ba huruminsa ba ne saboda ba shi ne likitan fadar shugaban kasa ba.
Wasu bayanai da suka bulla a ranar Asabar sun ce daga cikin wadanda suka kamu da cutar a fadar ta Villa, har da dogarin shugaba Buhari, wato Yusuf Dodo da babban jami’in tsaron fadar, Aliyu Musa.
An kuma ruwaito cewa Ministan Yada Labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed na cikin wadanda suka kamu da wannan shu’umar cuta, sai dai tuni ministan ya musanta hakan.
Aminiya ta ruwaito cewa, cutar ba ta yi wa wadannan jami’ai mugun kamu ba, la’akari cewa duk sun karbi cikakkiyar allurar rigakafinta.