✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An sallami mutum uku da suka warke a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sallami mutum uku bayan sun warke daga cutar coronavirus a jihar. Kwamishinar Lafiya ta jihar Dakta Amina Mohammed Boloni, ce ta…

Gwamnatin jihar Kaduna ta sallami mutum uku bayan sun warke daga cutar coronavirus a jihar.

Kwamishinar Lafiya ta jihar Dakta Amina Mohammed Boloni, ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai ranar Juma’a.

Ta ce, an sallame su ne bayan an yi masu gwaji biyu, wanda sakamakon ya nuna basu da kwayar cutar.

Mutum ukun da aka sallama na daga cikin mutane shida da ke dauke da cutar a jihar.

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar ta sallami mutum guda bayan shima ya warke.

A yanzu haka saura mutum biyu da ke dauke da cutar, wanda Kwamishinar  ta ce suna sa ran suma Allah Ya basu Lafiya.

A cikin makon nan ne Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai, ya sanar a shafinsa na Twitter cewa, har yanzu bai warke daga cutar ba.