Gwamnatin Jihar Legas ta ce an sallami majinyata biyar da suka warke daga cutar coronavirus ranar Litinin daga cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa da ke Yaba.
Kawo yanzu mutum takwas ke nan suka warke aka sallame su daga cibiyar.
Daya daga cikin majinyatan biyar ya shaida wa ‘yan jarida cewa ya shafe makwanni biyu ne a cibiyar, kasancewar ranar 15 ga watan Maris aka tabbatar masa yana dauke da cutar, inda aka bukaci ya dawo washe gari aka kwantar da shi.
“Da fari na fuskanci kalubale, amma daga baya al’amura sun daidaita, an ba mu kulawa sosai, Ni da ragowar majinyatan da aka sallama mun shaida hakan”, inji shi.
Ya kuma ce kada jama’a su tsorata domin da sannu za a shawo kan annobar, “za mu iya cin galaba a kanta, ina ba da tabbacin cewa ragowar da ke jinya ba za su dawwama a nan ba. Abin da suke bukata shi ne samun kwarin gwiwa su kuma sha maganin yadda ya kamata, cikin dan lokaci za su warke a kuma sallame su”.
Ya kara da cewa kamata ya yi gwamnatin jihar Legas da ta tarayya su bai wa jami’an kiwon lafiya kulawa ta musamman domin kara masu kwarin gwaiwar bai wa masu cutar Coronavirus kulawa, domin da ba don irin gudunmawar da suke bai wa majinyatan ba, da da dama sun mutu.
Majinyatan, wadanda a baya suka kasance a killace a cibiyar, suna cikin koshin lafiya sannan sun bayyana godiyarsu ga gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu.
Sun kuma bukaci a bai wa jami’an kiwon lafiya da ke aiki a cibiyar inshorar rai.