Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya sake tsawaita dokar kulle da mako daya,a yunkurin sa na kare yaduwar annobar coronavirus a jihar.
A sanarwar da gwamnan ya fitar a ranar juma’a, 15 ga watan Mayu, gwamnan ya shaida cewa za a ci gaba da daukar kwarara matakai domin jama’a su kiyaye dokar kullen, tare da yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci.
Yace za a kamar yadda aka saba a baya, za a sassauta dokar kullen a ranaikun Litinin da Laraba da kuma jJuma’a daga karfe 7 na safe zuwa 5 na yamma a tsawon makon da aka kara dokar kullen.
Dokar kullen ta cigaba da aiki a jihar Ogun tun bayan da shugaba Buhari ya bada umarnin sassauta dokar a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya, sai dai a jihar Ogun gwamna Dapo Abiodun ya ci gaba da sanya dokar kulle bayan da gwamnatin tarayya ta janye nata.