✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An dakatar da Sallar juma’a da taruka a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta shawarci shugabannin addini da su dakatar Sallar Juma’a da sauran salloli ta kuma bukaci malaman addinin Kirista su dakatar da gudanar…

Gwamnatin jihar Kaduna ta shawarci shugabannin addini da su dakatar Sallar Juma’a da sauran salloli ta kuma bukaci malaman addinin Kirista su dakatar da gudanar da ibada a coci ranar Lahadi da sauran tarukan addini domin kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

Wannan cikin matakin da Gwamnatin Kaduna ta dauka wajen rufe makarantu da suka hada da: naziri da Firamare da Sakandare da kuma manyan makaruntu na jami’o’i da dai sauransu da gwamnatin jihar ta sanar da zai fara daga ranar 23 ga Maris 2020. Har zuwa tsawan kwanaki 30.

Mai taimakawa Gwamna Nasir El-Rufai, a fannin watsa labarai  Muyiwa Adekeye, ya rattabawa sanarwar hannu.