Gwamnatin jihar Ogun ta dage dokar hana fita a jihar zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Afrilu 2020.
Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, ne ya sanar da hakan a yau Litinin a sa’ilin da yake rangadi a cibiyar killace masu ɗauke da cutar Coronavirus mai dauke da gadajen marasa lafiya 128 ta makarantar sakandare ta HID Awolowo da ke Ikenne a karamar hukumar Remo a jihar.
A ranar Lahadi ne shugaba Buhari ya sanar da umarnin rufe jihohin Legas da Ogun da birnin tarayya Abuja a lokacin jawabin da ya gabatarwa al’umar kasar.
Gwamnan jihar Ogun ya shaida cewa, ya tuntubi shugaba Buhari domin a dage dokar a jihar Ogun har zuwa ranar juma’a mai zuwa domin a bai wa al’ummar jihar daman shiryawa sossai kafin dokar hana fitar ta fara aiki.
Dapo Abiodun, ya ce shugaba Buhari ya gamsu da bukatar da ya kai masa, ya kuma yi na’am lamarin da ya sanya dage dokar har zuwa ranar Juma’a mai zuwa, inda ya bukaci al’umar jihar da suyi tanadi sosai kafin ranar da dokar zata fara aiki.
A yau Litinin kasuwannin jihar Ogun sun cika makil, inda jama’ar jihar suka yi ta tururuwa sayan kayan abinci kafin labarin dage dokar ya ta iske masu, jama’a da dama sun koka duba da yadda ‘yan kasuwa suka tsawwala farashin kayayyakin masa rufi da irin cunkoson da suka ga anyi a kasuwannin jihar.