Gwamnan jihar Oyo yace ayi wa matafiya 11 gwajin cutar COVID-19 kafin a koma dasu Sakkwato , jihar su ta asali.
A cikin daren ranar Juma’a da ta gabata ne ‘Yan Sanda a Jihar Oyo suka kama matafiya 11 da suka taso daga Sakkwato zuwa Akure bayan sun taka dokar hana tafiye-tafiye a tsakanin Jihohin kasa.
Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Oyo Mista Shina Olukolu da ya isa ofishin ‘yan sanda na Gbagi da aka fara tsare mutanen a ranar Asabar da safe, ya ce an kama su ne a qauyen Asejire dake kan iyakar Jihohin Oyo da Osun.
Daga bisani Gwamna Seyi Makinde ya jagoranci tawagar kwamitin yaki da cutar Coronaviru zuwa wurin da ake tsare da mutanen, a inda ya bayar da umarnin killace su da yi masu gwajin cutar kafin a koma dasu Sakkwato inda suka fito.
Gwamna Seyi Makinde, ya nuna mamakin yadda mutane suka taso daga Sakkwato suka tsallake wasu Jihohi a daidai lokacin da dokar hana tafiye-tafiye a tsakanin jihohin kasa take aiki.
Ya kars da cewa yanzu haka ya fara tuntubar takwaransa na jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a kan batun kama wadannan mutane a Jihar Oyo a irin wannan lokaci.
Direban motar dake xauke da mutanen, Muhammed Idris ya ce sun samu isowa wannan wuri ne (qauyen Asejire) bayan ketowa ta cikin dazukan wasu jihohi domin gujewa faxawa hannun jami’an tsaro.
Ana cigaba da samun matafiya daga Arewa zuwa Kudu ko kuma aka sin haka duk da dokar hana ficen da mahukunta suka gidanya domin kare yaduwar cutar a tsakanin jihohin Najeriya.