✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Copa del Rey: Gobe Sebilla za ta hadu da Barcelona a wasan karshe

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasan karshe na cin kofin Copa del Rey na Sifen a tsakanin  kungiyar kwallon kafa…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasan karshe na cin kofin Copa del Rey na Sifen a tsakanin  kungiyar kwallon kafa ta Sebilla da kuma ta FC Barcelona.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 8:30 na dare agogon Najeriya.  

A tarihin kofin, kulob din FC Barcelona ne ya fi kowane kulob a Sifen yawan dauka, inda kawo yanzu ya dauka har sau 29.  Kenan idan ya samu nasara a wasan gobe zai lashe kofin sau 30 kenan.  Kulob din Sebilla ya taba lashe wannan kofi ne sau biyar.  Kulob biyar da ke sahun farko wajen lashe wannan kofi su ne:  FC Barcelona mai 29 sai Atletico Bilbao ta biyu da kofi 23 sai Real Madrid a matsayin ta uku da kofuna 19 sai Atletico Madrid ta hudu da kofuna 10 sai balencia da ke matsayi na biyar mai kofuna 7.  Kulob din Sebilla ne yake matsayi na 7 da kofuna 5.

Tuni kocin Sebilla da na Barcelona suka kammala shirye-shirye don tunkarar wasan da ake sa ran dubban jama’a ne za su kalla kai tsaye da kuma a akwatunan talbijin a kowane sashe na duniya ciki har da Najeriya.