Cocin Katolika da ke jihar Filato ta ce ta karbi ban hakurin da Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya yi kan maganganun da ya yi lokacin aka nada shi, Daraktan yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC.
Archbishop na Cocin Katolika da ke Jos, babban birnin jihar Filato, Archbishop Rabaran Matthew Ishaya Audu je ya bayyana karbar yafiyar a madadin cocin.
- Alkawari daya ne ba mu cika wa Shekarau ba — Kwankwaso
- Motoci 10 da Buhari ya ba mu har yanzu ba su zo hannunmu ba – Nijar
Rahotanni sun nuna kalaman Gwamnan a kan takarar Musulmi biyu a jam’iyyar ba su yi wa cocin dadi ba.
Archbishop Matthew Ishaya Audu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron cocin na kasa karo na 19, da aka gudanar a Cocin Louis Parish da ke Jos.
Ya ce, “game da hakurin da ka bai wa wannan Coci, babban taron Bishop-Bishop na wannan Coci, karkashin jagorancin Shugabansu na cocin Katolika, ya amince tare da karbar wannan ban hakurin da ka yi.”
Ya kuma ce cocin na karfafa wa mabiyanta gwiwa kan su shiga harkokin siyasa.
Ya bai wa gwamnan tabbacin cewa cocin ba za ta ba shi kunya ko kuma ta bari ya fadi a wannan jagorancin da aka bashi ba.
Sai dai Achbishop din ya yi kira ga Gwamnan da ya bai wa babbar jam’iyya mai mulki ta APC shawara kan hadin kai tare da tafiya da al’ummar kasa baki daya.
A nasa jawabin, gwamna Simon Lalong ya ce yana biyayya da yin imani da kasancewa jakadan kwarai na cocin a duk inda ya tsinci kansa.
Ya ce dangane da maganar da ya yi, kwanakin baya, wadda ta kawo cece-kuce, bai kamata a ce za a yi masa hukumlnci kan soyayyarsa da biyayyarsa ga cocin da take koyar da yafiya ba.
“A duk inda hadin kai da soyayya da ci gaba suka samu, za mu iya yi wa ubangiji abubuwa masu kyau. Don haka, ina shawartar ’yan uwana ’yan siyasa mu rika yin koyi da abubuwan da wannan Coci take yi,” inji Gwamna Lalong.