✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ciyar da mahajjata zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya’

Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta ce ciyar da abinci ga mahajjatan Najeriya a Saudiyya a lokacin aikin Hajji za a iya amfani da shi…

Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta ce ciyar da abinci ga mahajjatan Najeriya a Saudiyya a lokacin aikin Hajji za a iya amfani da shi wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Kwamishinan Tsare-Tsare da Kula da Ma’aikata da Harkokin Kudi na  Hukumar NAHCON, Alhaji Yusuf Adebayo Ibrahim ne ya bayyana haka lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da ciyar da mahajjata da hukumarsa ke yi lokacin aikin Hajji, inda ya ce Najeriya za ta samu riba sosai  idan aka samu kyakkyawan tsari na shigar da abincin Najeriya zuwa kasar Saudiyya a lokacin aikin Hajji domin amfanin mahajjatan.

“Najeriya za ta iya cin riba sosai idan za a yi amfani da wannan dama yadda ya kamata. Za a iya shiga da abincin Najeriya zuwa Saudiyya a sayar ga masu dafa abincin da mahajjatan Najeriya ke ci a lokacin zamansu a Saudiyya don gudanar da aikin Hajji.  Ta hanyar yin haka, mun taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasarmu da kuma mai masaukinmu. Ku tuna galibin mahajjatanmu mazauna yankunan karkara ne da suka fi son abincinsu na gida, don haka ne masu sayar da abinci irin namu suke samun ciniki sosai a Saudiyya,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Kuma hakan zai sa masu dafa abincin su dauki ’yan Najeriya da suka san yadda ake dafa irin wadannan abinci domin sub a ’yan Najeriya irin dandanon abincin da suke so.” Kwamishinan ya yi kira ga hukumomin alhzai na jihohi su ba shirin ciyar da mahajjatan cikakken hadin kai domin amfanin kasar nan maimakon kawo kafar ungulu da wasu jihohi suka nuna.

Idan za a tuna ciyar da mahajjatan Najeriya a Makka da Madina da wurare masu tsarki (masha’ir) a baya ya hadu da cikas ta hanyar yi masa kafar ungulu da kazanta da kuma wahalhalu. A hankali a hankali ne aka bullo da tsararren shiri da aka daidaita shi wajen ciyarwar.  

A shekarun baya an rika ba mahajjata abinci sau biyu ne: Karin kumallo da kuma abincin dare a otel-otel dinsu. Kuma ana kokarin samar musu da irin abincin gida. Sannan Hukumar NAHCON ta umarci kwararrun masu dafa abinci su dauki masu dafa abinci ’yan Najeriya domin tabbatar da an dafa irin girnkin da ’yan Najeriya suke bukata yadda ya kamata tare dab a mahajjatan.