✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciwon Sikila ba lasisin mutuwa ba ne — Ƙwararru

Ƙungiyar Mirror Me ta nanata buƙatar canja tunanin jama’a game da cutar Sikila.

Ƙwararru a harkar kiwon lafiya sun ce, ciwon Sikila ba ya nuna alamun mutuwa don an kamu da shi.

Sun bayyana haka ne, a wani taro da aka gudanar a Abuja; don ƙoƙarin sauya tunanin mutane kan cutar a Ranar Tunawa da Sikila ta duniya.

Ƙungiyar Mirror Me da haɗin gwiwar Gehenesphere ne suka shirya taron, wanda ya bayar da haske kan makomar Kobiro Es- elemo, fitacce kuma jigo a cikin masu ɗauke da cutar Sikila.

Babban Jami’in Ƙungiyar Mirror Me da mai shirya taron, Daniel Ojo, sun nanata buƙatar canja tunani daga jama’a game da cutar Sikila.

“Cutar Sikila, ba ta nufin mutuwa yanzu,” Ojo ya bayyana.

Ya ce, “Wajibi ne, mu daina kallon masu ɗauke da cuta a matsayin raunana ko kasassu, domin suna da ƙarfi da juriya, kuma lokaci ya yi da al’umma za ta gane haka.”

Babban mai jawabi, Misis Olunaike, ta goyi bayan kalaman Ojo, inda ta nanata muhimmancin nuna hali mai kyau da kuma buƙatar tallafa wa waɗanda ke ɗauke da cutar Sikila.

Sai ta buƙaci ma’aikatan kiwon lafiya su kasance masu tausayi da tausayawa. Kuma marasa lafiya su guji amfani da jabun magunguna.

“Dole ne mu kawar da tatsuniyar da ke cewa, masu ɗauke da cutar Sikila na shan wahala wajen jinyarsu. Sannan, masu ɗaukar ma’aikata ma; dole ne su cire son zuciya wajen ɗaukar masu cutar Sikila aiki. Domin kuwa ko shakka babu, waɗannan bayin Allah na da dama tare da ’yanci kamar kowa,” in ji Olunaike.

Dokta Mista Ovye Ewuge wani ƙwararren likitan jini a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Keffi a Jihar Nasarawa, ya bayyana yadda za a kauce wa kamuwa da cutar da kula da masu ita yadda ya dace.

Sai  ya nuna muhimmancin neman kulawar likita, lokacin da ake cikin tsanani da tashin hankali; maimakon dogaro da magunguna kaɗai.