Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta doke abokiyar hamayyarta, Manchester United a kofin Community Shield.
Wasan ya kai ƙungiyoyin ga bugun fenareti bayan shafe minti 90 ana murza leda a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.
Ɗan wasan gaban Man United, Alejandro Garnacho ne ya fara jefa mata ƙwallo a minti na 82.
A minti na 89, Bernardo Silva na warware wa Manchester City ƙwallon da aka zura.
Hakan ne ya kai ƙumgiyoyin biyu bugun fenareti.
Mutum bakwai ne suka buga wa ƙungiyoyin biyu fenareti.
A ɓangaren Manchester City, Bernardo Silva ne ya zubar da fenareti, yayin da ɓangaren Manchester United, Jardon Sancho da Jonny Evans suka gaza saka ƙwallon a raga.
Hakan ne ya sa Manchester City ta zama zakarar Community Shield ta 2024.
A mako mai zuwa ne za a dawo buga gasar Firimiyar Ingila, bayan ƙarƙare kakar wasanni ta bara.