Fadar Shugaban Kasa ta ce sabanin yadda mutane da dama ke tunani, tarihi zai tuna da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi abin da ya dace wajen cire tallafin mai.
Kakakin Shugaban Kasar, Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.
- ’Yan Najeriya sun caccaki likin kudi a bikin Hanan Buhari
- Harin Boko Haram: Sojoji na cikin shirin ko-ta-kwana
- Matasa sun caccaki gwamnati kan karin farashin kaya
Ya ce tilas ce ke sawa a wasu lokutan a dauki tsauraran matakai kamar janye tallafin wasu abubuwa irinsu man fetur, wutar lantarki da takin zamani muddin ana so a dora kasar a kan tafarkin ci gaba mai dorewa.
Garba Shehu ya ce da hadin kan ’yan Najeriya, Buhari ya samu kwarin gwiwar daukar matakin, wanda ya yi amannar a karshe za su ci gajiyar shi.
Ya ce shugaban na duba abubuwan da za su kawo cigaba ne ba wai siyasa ba, musamman a lokacin nan da kasar ke cikin mawuyacin hali; yana mai cewa tarihi ba zai manta da Buharin ba, sabanin abin da ’yan adawa ke fada musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
Garba Shehu wanda ya ce babban abun da ake bukata a mulkin dimokuradiyya shi ne amincewar jama’a kuma shugaban ya same ta daga dukkannin ’yan kasa, ciki har da jam’iyyun adawa da kungiyoyin kwadago da na masu zaman kansu kafin daukar matakan.
Ya ce, “A kokarinmu na hana almubazzaranci da wuwuwurun dukiyar al’umma da sunan ba das tallafin man fetur, takin zamani da wutar lantarki, gwamnatinmu ta yanke shawarar zartar da maunfofin da aka dade ana jira domin a kyale yanayin kasuwa ya yi alkalancin yadda farashinsu zai kasance.
“Gwamnatoci da dama da suka gabata sun fahimci cewa cire tallafi a wadannan bangarorin shi ne zai zama maslaha tare da ciyar da kasar gaba a fannin tattalin arziki.
“Wadannan sauye-sauyen sun zama tilas kuma an dade ana jiran ganin ranar aiwatar da su”, inji Garba Shehu.