Gwamnatin Jihar Kwara ta rage kwanakin zuwa aikin ma’aikatanta a matsayin matakin wucin-gadi na rage musu radadin cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Shugabar ma’aikatan jihar, Misis Susan Modupe Oluwole, ta sanar cewar Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayar da umarnin rage kwanakin zuwa aiki zuwa kwana uku a mako ga kowane ma’aikaci.
- Rukunin farko na maniyyatan Kano sun tashi zuwa kasa mai tsarki
- ’Yan ta’addan ISWAP 82 sun nitse a ruwa suna kokarin tsere wa sojoji
Sanarwar da babban sakataren yada labarai, Murtala Atoyebi ya fitar, ta umarci dukkan shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da su gaggauta tsara yadda tsarin zai yi aiki.
Sai dai shugabar ma’aikatan ta gargadi ma’aikatan da kada su yi wasa da damar sannan ta jaddada cewa za a kara sanya ido kan vadda suke gudanar da ayyukansu domin tabbatar da bin doka da oda.
Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki aka fara samun dogayen layuka a gidajen mai, da kuma tashin gwauron zabon farashin man.
Hakan dai ya jefa mutane cikin tsaka mai wuya musamman a fannin sufuri.