Wata Babbar Kotun Abuja da ke zamanta a Apo, ta umarci Sanata Elisha Abbo da ya biya naira miliyan 50 a matsayin tarar cin zarafin wata mata da ya yi a wani shagon sayar da kayan wasanni na jima’i.
Lauyan da ke kare hakkin karar mai lamba FHC/CV/2393/19, Lugard Tare-Otu, ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter yana cewa Kotun ta umarci Sanata Abbo ya biya matar hakkin tozarcin da ya yi wa matar.
- Ana zargin matasa da kashe dattawa ta hanyar tsafi a Binuwe
- Cin zarafin da ’yan Afirka ta Kudu ke yi ga ‘yan Najeriya
A ranar 11 ga watan Mayun 2019 ne wata na’urar daukan hoton bidiyo ta nado Sanatan mai wakiltar shiyyar Adamawa ta Arewa a Majalisar Dattawa, yana ta marin matar, Osimibira Warmarte a shagon.
Cikin wani rahoto da sashen Hausa na BBC ya ruwaito, wasu bayanai sun ambato Sanatan cike da nadama yana neman gafara tare da neman a yafe masa da cewa ba halinsa bane tozarta mata.