✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin zarafin gidajen jaridu

A lokuta fiye da biyu Shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya so a ce shi shugaban kasa soja ne, sai dai a  makon jiya Shugaba…

A lokuta fiye da biyu Shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya so a ce shi shugaban kasa soja ne, sai dai a  makon jiya Shugaba Jonathan da mukarrabansa sun cika burinsu domin sun dauki mataki kamar na sojoji.
A wani mataki na allawadai da sojoji suka dauka, wanda kuma ya yi hannun riga da mulkin dimokuradiyya, sojoji suka tsare motocin da ke raba jaridu a wadansu manyan garuruwan kasar nan. A cikin gidajen jaridun da sojoji suka tsare motocinsu akwai Kamfanin Media Trust da ke buga jaridar Daily Trust da Aminiya da Weekly Trust da kuma Sunday Trust. Sauran gidajen jaridun da abin ya shafa sun hada da Leadership da The Nation da Punch da kuma banguard.
Rabon da aka ga irin wannan kama karya a kan ’yancin aikin jarida da kuma na tofa albarkacin baki tun kafin a sanya dokar ’yancin aikin jarida ta shekarar 1964, sai kuma irin yadda gwamnatin sojoji ta rika yi a wadansu lokuta. Abin takaicin shi ne, al’amarin da ya faru makon jiya, wanda ya faru a mulkin dimokuradiyya. A Juma’ar makon jiya ne aka ajiye sojoji a wadansu birane da kuma garuruwan kasar  don su duba dubban jaridun da aka buga, inda aka ci gaba da haka a ranar Asabar. A ranar Asabar din sojoji sun ci gaba da hana raba jaridun kasar nan a dukkan jihohin arewacin Najeriya da kuma Abuja.
Gidajen jaridu da sauran makaranta sun rika tambayar wane buri ake so a cimmawa wajen hana raba jaridun. Daraktan Yada Labaran Hukumar Sojoji Manjo-Janar Chirs Olukolade ya ce, wannan mataki ya zama dole ne, saboda sun samu bayanin ana amfani da motocin raba jaridu wajen daukar muggan makamai da bama-bamai. Ya tabbatar ba su dauki wannan matakin don dakile ’yancin fadar albarkacin baki da kuma ’yancin aikin jarida ba.
“Hedkwatar tsaro ba ta dauki wannan matakin sakamakon wani gilli da take da shi ga gidajen jaridu ba, ko don ta kawo tarnaki ga ’yancin aikin jarida ba. Sojoji suna yaba kokarin da gidan jarida suke yi wajen fadan da suke yi da ’yan ta’adda. Don haka sojoji ba za su dauki mataki da gangan don su dakili ’yancin aikin jarida ba.” Inji shi.
Babban abin dubawa a nan shi ne, sojoji ba su daina korafin rashin gamsuwa da rawar da ’yan jarida suke takawa wajen yaki da ta’addancin da sojojin ke yi ba. Kasancewar sojojin sun sha nanatawa cewa ’yan jarida su rika buga labarin bangarensu kawai, ba tare da fadar ainahin al’amarin da yake faruwa ba. Idan ’yan jarida za su ci gaba da buga ainahin labarin da yake faruwa, to kuwa a cewar sojoji hakan ya nuna ’yan jarida na goyon bayan ’yan ta’adda ne. Idan za a duba ra’ayoyin gidajen jaridar kasar nan, za a ga yadda suke bayanin yadda za a guji tashin hankali da zubar da jini.
Bayan an kammala duba motocin ba tare da an samu wani makami ko kayan laifi ba, amma sojoji ba su sake motocin ba sai bayan awowi. Wannan ya nuna akwai wani lauje cikin nadi, wanda babu mamaki ana so a kassara gidajen jaridun ne, ta hanyar a bar su su kashe kudinsu wajen buga jaridar, sannan sai a hana su sayarwa.
Wani abin daure kai shi ne, Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa ba ta hannu cikin matakin da sojoji suka dauka, sannan ya bukaci gidajen jaridu su yi hakuri da matakan da sojoji suka dauka. Wannan batu ya zama bakin ganga.
A wata sanarwar da Mai Taimaka wa Shugaban kasa na Musamman kan Harkokin Jama’a Doyin Okupe ya fitar, ya ce, batun wai Jonathan ne ya shirya hakan don a tsoratar da gidajen jaridu, musamman dangane da irin labaran da suke kawowa da suka shafi irin badakalar da ke faruwa a gwamnati ba gaskiya ba ne, “Rahotom da ake yadawa na cewa sojoji na tsare motocin raba jaridu don suna dauke da wadansu labarai ba gaskiya ba ne, illa an yi hakan ne sakamakon bayanin da jami’an tsaro suka samu cewa, ana amfani da motocin jarida wajen daukar muggan makamai da bama-bamai.”
Wani abu kuma mai daukar hankali shi ne, wata sanar da Hukumar da ke Lura da Wata Labarai ta Najeriya ta fitar ita ce, dole gidajen rediyo da talabijin su rika mika mata sunayen bakin da za su rika hira da su kai-tsaye kwana biyu kafin gabatar da shirin.  Babu wata kalma da za a yi amfani da ita wajen bayanin wannan al’amarin da ta wuce ‘tacewa karfi da yaji’. Dalilin haka ne ma hukumar ta dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’ da gidan rediyon bision Fm 92.1 (da ke Abuja) ke gabatarwa.
Yanzu cikin kasa da wata takwas kafin a gabatar da zabe, gwamnati tana so ta yi amfani da ikonta wajen dakile duk wadansu muryoyi da za su fadi gaskiya a kan duk wani abu da gwamnati ta yi ba bisa ka’ida ba, musamman ga gidajen watsa labaran da ba na gwamnati ba.
Dalilin da ya sa kungiyar Kafafen Watsa Labarai ta Najeriya da kungiyar Masu Kamfanonin Buga Jaridun suka fitar da wata sanarwa da ke jan hankalin gwamnati wajen dakile ’yancin aikin jarida, kungiyoyin sun yi allawadai wajen hana raba jaridun da sojoji suka yi, inda suka ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dimukuradiyya.
Don haka ya kamata gwamnati ta sanya sojoji su dakatar da abubuwan da suke yi wa gidajen jaridu, don hakan ba zai haifar da da mai ido ba, yaki ne da sojoji da gwamnati ba za su yi nasara ba.