Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Harkokin Rundunar Sojan Ruwa, Sanata Isah Hamma Misau, ya ce jami’an ’yan sanda na biyan kimanin Naira miliyan daya da rabi don samun karin girma na musamman ta hanyar Hukumar ’Yansanda ta Kasa.
Sanata Misau wanda har ila yau tsohon jami’in dansanda ne day a yi ritaya daga aiki, ya fada wa wakilinmu yayin da ya tuntube shi kan badakalar cin hanci da ta mamaye Hukumar ’Yan sanda Ta Kasa.
Wata majiya ta tsaigunta wa Aminiya cewa jami’an ’yan sandan na biyan kimanin Naira dubu 500 don samun karin girma na musamman wanda Hukumar ’Yansanda ta Kasa da ofishin Sufeto-Janar na ’yansanda ke gudanarwa.
Majiyar ta ce wadanda suka biya kudin ne kawai da wadanda ke kusa da manyan jami’an ’yansanda da kuma wadanda ke kusa da manyan ’yan siyasa ke cin moriyar karin girman.
“Kamata ya yi a ce karin griman na musamman ana samunsa ne saboda wata bajinta da kuma aiki tukuru da wani dan sanda ya yi, amma lamarin sai ya koma sai an biya kudi. Idan ba haka ba me ya sa jami’an ’yansanda wadanda suke aiki a Arewa Maso Gabas ba su cin moriyar shirin? Kuma me ya sa wadanda suke cin moriyar karin girman wadanda suke kusa da manyan jami’ai ne ko kuma manyan ’yan siyasa”. Inji majiyar.
Amma da aka tambaye shi kan batun, Misau sai ya ce “Kana zancen Naira dubu 500, ai kudin ya fi haka. Wani jami’in dan sanda da ke aiki shi ya gaya mani cewa suna biyan kimanin Naira miliyan daya da rabi kafin su sami karin girma na musamman. Wasu majiyoyin sun tabbatar mani da haka. Saboda haka gaskiya ce tsagwaronta kawai”. Inji shi
A hannun daya kuma Hukumar ’Yan sanda ta Kasa (PSC) ta musanta rahoton cewa jami’anta na karbar na-goro daga hannun ’yan sanda don yi musu karin girma.
Mai Magana da Yawun Hukumar ’Yan sandan, Ikechukwu Ani ya ce “Ba gaskiya ba ne, hukumar ba ta taba karbar na-goro don karin girma ga wani dan sanda ba”.