✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin-bin-kwalam

Cin-bin-kwalam, kalami ne da na jiwo daga bakin wata ’yar dugwi-dugwi a lokacin da ta yi wa wasu sa’o’inta kwalelen kayan kwalam da makwalashe. Mu…

Cin-bin-kwalam, kalami ne da na jiwo daga bakin wata ’yar dugwi-dugwi a lokacin da ta yi wa wasu sa’o’inta kwalelen kayan kwalam da makwalashe. Mu dai a zamaninmu in muna son hana mai kwalama cin-cin da kwalam da makwalashe, sai mu nuna wa mutum sannan mu ce kwalelenka. Sai dai wani abin ban ta’ajibi ’yan dugwi-dugwi a wannan zamanin cewa suke yi, “Cin-bin-kwalam.”
Kayan kwalam da makwalashe da aka saba ta’ammali da su, sun hada da iloka da allagira da acamo da ’yar canai da alkaki da nakiya da gireba, Kai har ma da gullisuwa mai iya haifar da ’yar lisuwa. Wadannan kayan mayar da miyau da na jero duk mun saba dundume kururunmu da su, duk da cewa ba a cika yi musu cin tuwo ba. Sai dai a wannan zamanin taliyar indon-mami ta samu karbuwa a tsakanin ’yan dugwi-dugwi da ke halartar wuraren koyon watsattsake da buda wagagen littattafai, tun daga wurin shan fura-mai kyau, har zuwa jam’in jama’a a jami’o’in kasar Haurobiya. Hatta al’ummar gari sukan ziyarci teburin mai shayi, don dundume kururu da taliyar Indon-mami, har ma su kandami kokon Turawa, musamman ma a Haurubja, babban birnin Haurobiya.
Can kuwa a rukunin wadanda ba sa yin bobo da kwambon bokoko, akwai masu kwalama da kwaraka da zari, musamman in sun samu abin zurarawa a cikin tumbi don shawo kan tabahuwa, har ma su mangari ’yar Gusau  da ke karairaya da walankewa a kururun al’umma. Abin da ya sa al’umma ke afkawa cikin wannan mawuyacin hali, shi ne ‘jimiri da jinkirin cin jinbiri,’ a daidai lokacin da ake tsuwurwurta tsarin damo-da-kura-da-diyya.
Su kuwa ’yan watanda da suka saba wadaka da fantamawa a duk lokacin da suka wawushe lalitar kasar Haurobiya, sun saba haurawa kasashen ketare, inda sukan ketare da dami, har a tabbatar da cewa su manyan ’yan fashi da mukami ne. Irin wadannan rukuni na al’umma a cikin su ake samun samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, wadanda ba kayan kwalam da makwalashe ne a gaban su ba, domin su manufar su tsiyata kasa, su mayar da kowa bawa, ta yadda duk sa’adda aka kada kugen wasan Samson-siya-siya a dama-dama-da-kurda-kurdar siyasa, su ne masu hura firiki da horar da ’yan wasa, ta yadda da an doka ta-mola gidan talakawa kawai za a ci. Don haka duk sa’adda aka yi gasar harbatta-Mati ’yan fashi da mukami kle lashe modar gasar. Ana cikin wannan tabargaza da baranbarama da barusa, sai Mai-duka, Maikowa, Maikomai ya kawo mana Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo, su kuma suka nada Iro Mugun madambaci, don ya shako musu wuyan masu magu-magu.
Tunda Iro Mugun Madambaci ya fara cafke Samarin-kusu da ’yan matan jaba da gafiya, inda aka rika shakar wuyan su, har wasu sun amayar da dan abin da suka wawura, sai na fasko cewa ashe Gwamnatin Jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu ta dauki salon ’yan dugwi-dugwi wajen taka wa mahandama burki. Domin mun fuskanci cewa duk wanda ya ci acamo daga rumbun dukiyar Haurobiya Baban-burin-huriyya ya ce a cacimo shi, wanda kuwa ya dundume kururunsa da gullisuwa, to sai a yi masa gwale-gwale har ’yar lisuwa ta kama shi. Wanda kuwa ya yi yunkurin kwasar gireba, zai shiga gararamba, domin babu sauran gararuma, ballantana a yi kwalema. kuda dai an ce ‘wajen kwadayi a kan mutu,’ inji Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare das a-in-sa ba.
Batu na ingarman kwangiri, al’amuran da ke faruwa a kasar nan na nuni da cewa hukumomi sun ce, ‘CIN-BIN-kWALAM!’
Masu cabin cin bobo da kwanbon bokoko sai ku taka kahan-kadaran. Domin karo da Iro Mugun Madambaci babu dadi. Mun dai ga yadda aka karke da Mace-da-zane ga Samun-bom-da-sauki ga Santala kwadaiduwa da Asarar-dan-kwabo da Tumfafin-falo, har ma da In-gwan-gwaje-in-wala, wadda ta rike musu kahon nagge suka yi ta tatsar nonon nagge da karsana; da sauran jiga-jigan jigata al’umma a Gwamnatin Gudun-loko karkashin jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da suka jirga Haurobiyawa, wadanda suka yi zari-ruga, gafiya ki tsira da na bakinki. Wannan karon dai an ce lallai sai “kura ta amayar da abin da ta ci, ta hadidiye.”
Masu handama da babakere, wadanda suka yi tauna cinye ka hadidiye, an mayar amusu da martani, wato dai CIN-BIN-kWALAM. Baya ga takun mahukuntan Haurobiya, wadannan masu tsuwurwurta mugun aiki sun hadu da taskun dafdalar daular Dala. Sannan ga batan dabon kundin baje kolin Hauro na shekarar dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, al’amarin da sai kwanannan aka kawo karshen turka-turkarsa. Uwa-uba miyagu sun hadu da sasarin lalita guda da Baban-burin-huriyya ya kakaba musu, inda ya umarci kowane ofishin da masu laluben ladar kwadago da la’adar kadago ya adana ’yan matsabbansa a ciki. Wannan lamari dai bai yi wa miyagu dadi ba. Kundin labaran da, da na yanzu zai ci gaba da nazarin tabargazar da miyagun Haurobiya suka aikata, musamman wadanda suka tafka ta’asa a kwanon tasa.
Mu dai muna nan a teburin dan Madamin kokon Turawa, inda muke kwankwadar gahawa da nau’ukan kayan shayi mai dandano da kamshin kayan yaji. Kodayake Maidamu yana cakuda taliyar Indon-mami ni dai ba na dundume kururuna da zaren alkama, sai dai taliya ’yar italiya.
A matsayina na Katafaren Direban allin wannan makaranta, zan karkare batutuwan wannan makon tare da jan na-zomon Saurayin-kirinki kan lallai ya yi kokarin zama Saurayin-kirki, musamman ganin yadda Hukumar Kwaram-kwandam ke kwaramniya da shi. Sannan ga jifa-jifan jifar hanyar da ya cefano wa ’ya’yan majalisar tsofaffin Haurobiya. Kaima Dogarin Wakilan Rafkiya ba zan kyaleka, tabbas akwai bukatar ka taka wa wadanda suka jagwalgwala mana kundin baje koli burki, tunda dai ta tabbata Baban-burin-huriyya ya goge cushen da suka yi masa, kuma tabbas za a turo Iro Mugun Madambaci ya yi gwagwa da ku a Hukumar Gwagwarmaya da masu fashi da mukami ko da dabara. Ni dai na ce muku CIN-BIN-kWALAM!