A yau Juma’a ne ake sa ran cibiyar ladabtar da matasa masu shaye-shaye da kuma koya musu sana’o’i (Nigas Rehabilitation and Skill Akuisition Centre) da aka fi sani da Cibiyar Malam Niga da ke Layin Soba a Rigasa Kaduna za ta fara sayar da jaridar Aminiya.
Shugaban Cibiyar Malam Lawal Maduru ya ce sun yi sha’awar sayar da jaridar ce ganin yadda babu wani takamaiman wurin da ake sayar da jaridar a yankin Rigasa da kewaye. Hakan ta sa masu bukatar sayen jaridar sai sun yi tafiya mai nisa kafin su samu kwafenta.
Ya ce yanzu masu sha’awar jaridar musamman wadanda ke zaune a yankin Rigasa za su iya samunta cikin sauki ba tare da sun yi tafiya mai nisa ba. Ta ce ganin yadda jaridar ta karbu a cikin al’umma musamman wajen samar da labarai masu ilimantarwa da nishadantarwa da kuma fadakarwa ta sa cibiyar yanke shawarar yin hulda da jaridar ta Aminiya.
Daga nan sai ya yi kira ga duk masu bukatar jaridar musamman wadanda suke zaune a yankin Rigasa da kewaye su garzaya Layin Soba wanda aka fi sani da Layin Malam Niga don sun sayi jaridar cikin sauki.
“Insha Allahu daga yau Juma’a za mu fara sayar da jaridar Aminiya a cibiyarmu da ke Layin Malam Niga, kuma muna fata masoya jaridar musamman wadanda suke zaune a yankin Rigasa za su yi amfani da wannan dama don ganin sun samu jaridar cikin sauki,” inji Sheikh Lawal Maduru, shugaban cibiyar.
Cibiyar Malam Niga za ta fara sayar da jaridar Aminiya
A yau Juma’a ne ake sa ran cibiyar ladabtar da matasa masu shaye-shaye da kuma koya musu sana’o’i (Nigas Rehabilitation and Skill Akuisition Centre) da…