✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cibiyar Bunkasa Ci gaban Jama’a ta tattaro ’yan kasuwa don gudanar da taron bita kan sana’o’i

Cibiyar  Bunkasa Ci gaban Jama’a (CHRD) ta Jami’ar Karatu Daga-Gida ta Najeriya (NOUN), ta gudanar da taron kara wa juna sani na wuni biyu ga…

Cibiyar  Bunkasa Ci gaban Jama’a (CHRD) ta Jami’ar Karatu Daga-Gida ta Najeriya (NOUN), ta gudanar da taron kara wa juna sani na wuni biyu ga masu hannu wajen bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan, domin ganowa da karfafa harkokin sana’o’i da kasuwanci.

Taron bitar wanda ya gudana a Tsangayar Kaduna na Jami’ar, Daraktan Cibiyar Farfesa Grace E. Jokthan ce ta bude shi, inda a jawabinta ta ce, an dora wa cibiyar alhakin gina harkokin kasuwanci irin na kasashen duniya da suka ci gaba.  

Ta ce, babbar mnufar bitar ita ce a karfafa tare da dada zurfafawa da samar da abu mai amfani ga masu ruwa-da-tsaki da abokan hadin gwiwa ta hanyar hadin gwiwa da niyyar inganta rayuwa masu sana’o’i da harkokin kasuwanci a fadin kasar nan.

Farfesa Jokthan ta ce, cibiyar tana da burin karfafa wa dalibai da masu samun horo gwiwa a matsayin wwata hanya ta samar da aikin yi da kuma zama wakilan kirkiro abubuwa domin su kasance masu kazar-kazar tare da bayar da gudunmawa ga ci gaba ba kawai ta hanyar samun kudi ba, har ma da sadaukar da kai wajen auna abubuwan da za su taimaka wa kasar nan.

Ta bayyana wa mahalarta cewa wani bangare na dalilin shirya taron bitar, shi ne a kara zaburar da su su dada zage dantse kan harkokin sana’o’insu tare da karfafa wa jama’a su rika kirkirowa da kuma jawo mutane su rika shiga shirin da tsarin ta yadda za a bunkasa zuba jari bisa dogaro da masu gudanar da harkoki da za su samar da dama ga wadanda suka kammala makarantu da dalibai su inganta kwazonsu.

An gudanar da zaman bita sau biyu, na farko a karkashin shugabancin Dokta Nuhu Lawrence Garba, Daraktan Cibiyar Karatu ta Kaduna, na biyu kuma a karkashin shugabancin Malam Ishaku Ali, Daraktan Kamfanin Tuntuba na TbET Consultants. 

Taron bitar wanda aka gabatarb da takardu hudu kan bunkasa sana’o’i da kasuwanci ya samu halartar wakiliyar Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC), Dokta Esther Orji da wakilin Gwamna Jihar Kaduna, Malam Hafeez Bayero da Manajan Daraktan Bankin Bayar da Rancen Sana’o’i da Kasuwanci na Jami’ar NOUN, Malam Usman Shehu Abba da sauransu.