✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chicharito ya koma West Ham United

Tsohon dan kwallon Manchester United na Ingila da Real Madrid na Sifen Jabier Hernandez da aka fi sani da Chicharito ya sanya wa kulob din…

Tsohon dan kwallon Manchester United na Ingila da Real Madrid na Sifen Jabier Hernandez da aka fi sani da Chicharito ya sanya wa kulob din West Ham United na Ingila hannu a kwantaragin shekara biyu kamar yadda rahotanni suka nuna.

A ranar Litinin da ta wuce ne dan kwallon mai kimanin shekara 29 ya sanya wa kulob din hannu a kan Fam Miliyan 16 kwatankwacin Naira Biliyan 7 da miliyan 264.

Chicharito, dan asalin Meziko da yanzu haka yake kwallo a kulob din Bayer Leberkusen na Jamus, tuni ya tattara kayansa  ya koma Ingila don ci gaba da kwallo a kulob din West Ham United.

Chicharito dai shi ne dan kwallon da ya fi kafa tarihi a Meziko a matsayin wanda ya fi zura wa kasar kwallaye a raga kuma ya nuna farin cikinsa game da yadda ya samu nasarar canza sheka zuwa kulob din West Ham.

“Na yi matukar farin ciki da na sake komawa Ingila don bugawa West Ham United kwallo, kuma gasar firimiyar Ingila ita ce gasa mafi zafi da armashi a duk fadin duniya”, in ji shi.