✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea: Tara ‘yan wasa masu kyau ba shi ke kawo nasara ba —Klopp

Chelsea za ta ji dadi daga karshe kuma za su yi karfi a shekara mai zuwa.

Kocin Liverpol Jurgen Klopp ya bayyana cewa yana jin dadi sakamakon gwagwarmayar da ya ga Chelsea tana yi bayan kashe kudi domin sayen ’yan wasa.

Duk da ’yan wasa 16 da kulob din ya saya, hakan bai taimaka wa kungiyar ba wurin samun nasarori ba zuwa yanzu.

Chelsea dai na fuskantar babban kalubale ganin cewa ta dade ba ta yi nasara a wasannin da ta buga ba a ’yan kwanakin nan karkashin jagorancin Graham Potter da Frank Lampard.

Chelsea dai na ci gaba da gwagwarmaya inda a halin yanzu kulob din yake mataki na goma sha biyu a teburin Firimiya, haka kuma Liverpool da ke na biyar a teburi na gaban Chelsea da maki 17.

A yayin da yake tattaunawa da Sky Sports, Klopp ya bayyana cewa, “ina ji wa Chelsea maganar gaskiya, saboda abubuwa ba su tafiya daidai.

“Ina ganin suna cikin kulob din da ke sama amma a dayan bangaren ba zai yiwu ka kawo kwararrun ‘yan wasa ba ka tara wuri daya kuma ka yi tunanin komai zai tafi daidai,” in ji Klopp.

Klopp ya kara jaddada cewa ba tara ‘yan wasa masu kyau bane nasara, akwai bukatar a gina tawagar ‘yan wasa.

“Ba zai yiwu kana da dakin sauya kaya biyu, ba kuma zai yiwu ka iya yin atisaye a fili biyu ba, dole ne ka hada abota da kuma samar da tawaga mai cike da karasashi, shi ya sa nake jin dadi.

“Chelsea za ta ji dadi daga karshe kuma za su yi karfi a shekara mai zuwa, amma ina kawo wannan ne kawai a matsayin misali,” in ji Klopp.