✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Chelsea ta dauki Christopher Nkunku daga Leipzig

Dan wasan zai fara murza wa Chelsea wasa a kakar wasanni mai zuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, ta cimma matsaya da RB Leipzig kan daukar dan wasanta Christopher Nkunku.

Tun a watan Satumbar wannan shekara ne likitocin Chelsea suka gwada lafiyar dan wasan.

RB Leipzig da Chelsea sun cimma yarjejeniyar ce kan Yuro miliyan 60, sai dai an karkare komai kan Yuro miliyan 70, sakamakon wasu tsarabe-tsarbe da Chelsea za ta biya.

Nkunku ya amince zai rattaba hannu kan yarjejeniyar zama a kungiyar na tsawon shekaru wanda zai ba shi damar murza leda yadda yake so.

Duk kungiyoyin sun amince da kulla yarjejeniyar, inda a yanzu kawai suke jiran lokaci da za a bude cinikayyar ’yan wasa don sanya hannu kan takardun da suka dace kafin sanar da komai a hukumance.

Ana sa ram dan wasan zai koma Chelsea a watan Yunin 2023, bayan an kammala kakar wasanni ta bana.