✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CHAN 2016: Gobe za a yi wasan kwata-fainal amma babu Naje

A cigaba da fafatawa a gasar cin kofin matasa na Afirka da ake fi sani da CHAN 2016 da yanzu haka yake gudana a Ruwanda,…

A cigaba da fafatawa a gasar cin kofin matasa na Afirka da ake fi sani da CHAN 2016 da yanzu haka yake gudana a Ruwanda, a gobe Asabar 30 ga Janairun, 2016 ne ake sa ran za a buga wasan kusa da na karshe watau Kwata-Fainal.  Sai dai daga cikin kungiyoyi takwas da suka haye zuwa wannan mataki na kwata-fainal babu Najeriya a ciki.
kasar Guinea ce dai ta yi waje da Najeriya a gasar a ranar Talatar da ta wuce bayan ta lallasa ta da ci aya mai ban haushi.
kungiyoyin da suka haye zuwa wannan mataki sun haa da mai masaukin baki Ruwanda da Dimokuraiyyar Kongo (Congo Dr) da Kamaru da kuma Kwaddebuwa.  Sauran su ne Gini da Tunisiya da Zambiya da kuma Mali.
Wasannin da za a yi a gobe sun haa da na Ruwanda da Dimokuraiyyar Kongo da misalin karfe huu na yamma agogon Najeriya sai wasa na biyu da ya kunshi Kamaru da Kwaddebuwa da misalin karfe bakwai na dare agogon Najeriya.
A jibi ne kuma Mali za ta kece raini da Tunisiya yayin da a wasa na biyu za a kece raini a tsakanin Zambiya da Guinea.
Duk kungiyoyin da suka samu nasara a wasannin su ne za su haye zuwa matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.
Tun bayan da aka fitar da Najeriya daga gasar ce koci Sunday Oliseh da kuma ’yan wasansa suke ta samu suka daga magoya bayan kungiyar Super Eagles a ciki da wajen Najeriya.  Hasalima waansu magoya baya sun  yi kiran a kori Sunday Oliseh a matsayin koci yayin da waansu kuma suke da ra’ayin a kara wa kocin wa’adi, kada a yi gaggawar sallamarsa.
Jim kaan da kammala wasan ne aka ruwaito Koci Sunday Oliseh ya aika wa magoya bayan kungiyar sakon bayar da hakuri a kan abin da ya faru.  Kocin ya nuna da ma tun farko bai kama kafar kowa ba kafin Hukumar NFF ta auke shi a matsayin kocin kungiyar da hakan ya nuna ko da an kore shi ba zai damu ba.
Sai dai wani rahoto da muka samu ya nuna ’yan kwallon Super Eagles sun buga wasa da Gini ne a ranar Talatar da ta wuce ba tare da sun ci abinci ba saboda Hukumar NFF ba ta aika musu alawus-alawus insu a kan lokaci ba.  Hakan ta sa koci Samson Siasia ya bayyana ’yan kwallon tamkar mota ce da babu mai a cikinta tun kafin a buga wasan.
A halin yanzu dai an fitar da Najeriya daga gasar sai kuma bai idan Allah Ya kaimu.