Saboda kokarin da ’yan kwallon Dimokuradiyyar Kongo suka yi na sake lashe Gasar cin kofin matasa na Afirka a karo na biyu a ranar Lahadin da ta wuce a kasar Ruwanda bayan sun lallasa Mali da ci 3-1 a wasan karshe, Shugaban kasar Joseph Desire Kabila ya yi wa ’yan kwallon da jami’ansu ruwan motoci inda ya ba kowane daga cikinsu mota kirar Jeep Prado.
Haka kuma shugaban ya ba kowane daga cikinsu kyautar Dala dubu 60 da ta yi daidai da Naira Miliyan 18 da dubu 600.
Shugaban ya ba kowane daga cikin ’yan kwallon da jami’ansu mabudan motocin da kuma cekin kudin da kansa ne a wani bikin karramawa da ya shirya musu jim kadan bayan sun koma kasar daga Ruwanda.
Dimokuradciyyar Kongo dai ta lashe kofin CHAN ne sau biyu a cikin shekara bakwai na tarihin gasar.
A gasar, Dimokuradiyyar Kongo ta samu rashin nasara ne a wasa daya kacal ne a zagayen farko bayan Kamaru ta doke ta da ci 3-1.
Sai dai a sauran wasannin da suka biyo baya kasar ta samu nasara akan Ethiopia da ci 3-0 yayin da ta doke Angola da ci 4-2.
A matakin kusa da na karshe (kwata-fainal) kuma ta doke mai masaukin baki Ruwanda da ci 2-1 kafin ta doke kasar Guinea a matakin semi fainal da ci 5-4 a bugun fanariti.
dan kwallon Dimokuradiyyar Kongo Mechak ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon gasar bayan ya zura kwallaye hudu a raga a gasar. dan kwallon Najeriya Elbis Chison Chikarata da dan kwallon Tunisiya Ahmed Akaichi su ma sun samu nasarar zura kwallaye hur-hudu yayin gasar.
A halin yanzu Dimokuradiyyar Kongo ta kafa tarihin kasar da ta lashe gasar har sau biyu.
Kenya ce za ta dauki nauyin gasar CHAN da za ta gudana a shekarar 2018.
CHAN 2016: An yi wa ’yan kwallon Dimokuradiyyar Kongo ruwan motoci
Saboda kokarin da ’yan kwallon Dimokuradiyyar Kongo suka yi na sake lashe Gasar cin kofin matasa na Afirka a karo na biyu a ranar Lahadin…