Gwamnatin Sojin Chadi ta sanar da dakile wani yunkurin juyin mulki a kasar wanda wasu manyan Sojoji da kuma wani fitaccen dan rajin kare hakkin dan adam suka shirya.
Sanarwar da gwamnatin Chadin ta fitar ta bayyana cewa manyan sojojin 11 da kuma Baradine Berdei Targuio, Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasar ne suka kitsa yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba.
A cewar kakakin gwamnatin Chadi, Aziz Mahamat Saleh an kame mutanen tun bayan 8 ga watan Disamban bara kuma tuni aka bude bincike na musamman a kansu game da tuhume-tuhume masu alaka da karya dokokin Kundin Tsarin Mulki da hada baki wajen aikita laifi baya ga mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma kalubalantar gwamnati.
Aziz Mahamat ya ci gaba da cewa, tuni kotu ta yi umarnin ci gaba da tsare su yayin da ake ci gaba da fadada bincike don gano sauran masu hannu da kuma gurfanar da su gaban kotu don amsa laifukansu.
A cewar gwamnatin karkashin jagorancin Mahamat Idris Deby tana yin taka-tsan-tsan wajen karin haske ga jama’a kan ayyukanta da kuma nauye-nauyen da ke kanta don wayar da kan jama’a.
Tun bayan mutuwar Idris Deby Itno a watan Aprilun 2021 ne Mahamat Idris Deby ke jagoranci kasar said ai y ana ci gaba da fuskantar bore musamman bayan matakin babban taron kas ana kara masa wa’adin tafiyar da mulki sabanin alkawarin da ya dauka na mika mulki ga fararen hula cikin kasa da shekaru 2.
Ko a watan Oktoba wata zanga-zangar kin jinin gwamnati sai da ta kai ga kisan mutane 50 cikin har da jami’an tsaro 10 yayin da aka kame wasu mutum 601 ciki har da kananan yara 83 tare da garkame su a gidan yarin Koro Toro mai nisan kilomita 600 daga birnin Ndjamena fadar gwamnatin kasar.