✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ce-ce-ku-cen Buhari da matarsa ba dabi’ar Musulunci ba ce – Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya ce cece-ku-ce a tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da matarsa A’isha Buhari a kan batun zargin…

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya ce cece-ku-ce a tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da matarsa A’isha Buhari a kan batun zargin wadansu ke juya gwamnatinsa ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Alhaji Balarabe Musa wanda ya bayyana haka a zantawarsa da Aminiya a Kaduna ya ce bai dace Shugaba Buhari da mai dakinsa su rika fitowa duniya suna cece-ku-ce a kan batun mulki ba.

Ya ce a Musulunci bai dace ba mata da miji su rika irin wadannan kalamai a bainar jama’a musamman kasancewarsu shugabanni.

“Wannan ya sa na ce da kai a tsarin Musulunci hakan da suka yi bai dace ba. Zargin da matar ta yi da kuma amsar da Shugaban Kasar ya bayar, a matsayinsu na mata da miji akwai wasu abubuwa da ba su kamata su fito waje suna fadi ba. Wannan ba koyarwar Musulunci ba ne ba ma ga mata da miji ba hatta a tsakanin abokai,” inji shi.

Tsohon Gwamnan ya kuma shawarci ’yan Najeriya su kauce wa saka baki a wannan danbarwa a tsakanin mata da miji.

Game da ko zai ba da shawara ga Shugaba Buhari sai ya ce “Ni ba ni da wata shawara da zan ba shi, domin akwai ’yan Najeria da suka fi ni da za su iya ba shi shawara. Ni dai kawai na san wannan ba dabi’ar Musulunci ba ce,” inji shi.

Idan ba a manta ba Matar Shugaban Kasar A’isha Buhari ta yi zargin cewa wasdansu mutum biyu zuwa uku ne ke juya gwamnatin Shugaban amma ba shi ke mulki ba. Shi kuma Shugaba Buhari sai ya kalubalance ta da ta fito da sunayen wadanda ta ce suke juya shi a kan mulki.