✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ce-ce-ku-ce kan wanda ya yi garkuwa da Daliban Kankara

Yadda kawuna suka rabu har tsakanin masana harkar tsaro game da sace Daliban Kankara

Bayan an sako daliban Makarantar Kankara da aka yi garkuwa da su, jama’a na ta diga ayar tambaya a kan bayanan da suka gabaci sako yaran.

Jama’a daga bangarori daban-daban na jinjina bayanan da ke karo da juna ko daure kai tsakanin kungiyar Boko Haram da ta yi ikirarin garkuwa da su har ta fitar da bidiyon hakan.

Masana harkar tsaro dai sun yi ittifakin cewa tabbas kungiyar ce ta fitar da bidiyon ikirarin garkuwa da yaran.

A gefe guda kuma gwamnati ta musanta cewa kungiyar ta dauke  daruruwan daliban.

Shugaba Buhari yana yi wa Daliban Kankara jawabi a Katsina

Kazalika wasu kwararru a fannin tsaro sun bayyana tababa kan mutumin da ya yi jawabin sace yaran a cikin bidiyon Boko Haram wanda suka ce muryarsa ta dan bambanta da na Abubakar Shekau, shugaban Kungiyar.

Sun ce mai jawabin ya gabatar da kansa da sunan Abubakar Shekau, sabanin yadda Shekau ke gabatar da kansa da sunan Abu Muhammad Asshakawiy.

Mutumin a cewarsu, ya kuma daburce a wajen ambaton sunan kungiyar, wato Jama’atu Ahlissunnah Lidda’awati Wal Jihad.

Amma sun yi ittifaki cewa sakon na Boko Haram ne, har suka bukaci gwamnati ta gaggauta daukar mataki kafin kungiyar ta samu damar sulalewa da yaran zuwa Dajin Sambisa ko na Alagarno.

Tun a wancan lokacin sojoji da gwamnatin Jihar Katsina sun karyata ikirarin da ke cikin bidiyon na Boko Haram.

Sojoji sun ce farfagandar kungiyar ce kawai, yayin da Gwamnan Katsina, Aminu Masari ya ce masu garkuwa da mutane ne suka sace yaran kuma an fara tattaunawa da su don su sako su.

Bidiyo na biyu

Daga baya sai ga wani bidiyo dauke da tambarin Boko Haram yana nuna daliban, daya daga cikinsu na jawabi a madadin ragowar inda ya zayyano bukatun kungiyar.

Masharhanta sun ce bukatun da aka gabatar sun cakuda na Boko Haram da kuma na ’yan bindiga.

Bukatun su ne a rufe makarantun boko, a daina turo sojoji da jiragen yaki suna sintiri a cikin daji, sannan a rusa ’yan banga da ’yan kato da gora.

A bidiyon an ga yara da yawa suna rokon a kawo musu dauki, wadanda aka ce yawansu ya kai 520, adadin da ya zo daidai da wanda wani dalibi da ya tsere daga hannun ’yan bindigar ya bayar.

Sako dalibai 344

Bayan ikirarin da aka yi a bidiyon na biyu cewa Boko Haram ce ta sace yaran, a ranar ce kuma aka sako su.

Gwamatin Zamfara inda aka kubatar da yaran da ta Katsina inda aka sato su sun ce ’yan bindiga Fulani ne suka sako yaran.

Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce sulhu aka yi da ’yan bindigar kafin a karbo yaran su 344.

Matawalle ya ce a hannun Fulani ’yan bindiga aka karbo yaran ba a hannun kungiyar Boko Haram ba.

Ya ce an cimma nasara ne bayan amfani da sarakunan Fulani da tsoffin shugabannin ’yan bindiga wurin tattaunawar sulhun, inda ’yan bindigar suka lissafo matsaloli da aka yi musu alkawari za a sasanta.

Ya ce Fulanin sun nemi a tabbatar da cewa jami’an tsaron sa-kai, ’yan kato da gora da ’yan banga sun daina cin zarafinsu ko kashe musu shanu.

Yaron da ya yi jawabi

Bayan an sako yaran, wanda ya yi bayani a bididyon da masu garkuwar suka yi ya bayyana shakku cewa ’yan Boko Haram ne suka dauke su.

Ya ce mutanen ne suka sa shi ya ce su ’yan Boko Haram ne, ya kuma fadi bukatun da ya ambata; sai dai ya ce ya lura a firgice suke, kuma da wuya idan ’yan Boko Haram ne.

Daliban Kankara a lokacin da aka dawo da su Katsina bayan ‘yan bindida sun sako su.

Jama’a dai na ganin cewa maganar gwamnati ita ce abin dauka idan aka hada da ta yaron da kuma batutuwan da masana tsaro suka bayyana.

A wurin wasu kuma, idan har hakan ta tabbata, to akwai ayar tambaya game da yadda al’amarin ’yan bindiga ya dauko sabon salo, wato yin bidiyo domin gabatar da bukatu.

Bugu da kari akwai ayar tambaya kan yadda Boko Haram ta yi ikirarin sace yaran. Shin Boko Haram ta fara hada kai da ’yan bindiga ne, ko kuma ’yan bindigar ne suka koma yin ungulu da kan zabo da sunan Boko Haram?

Ala ayyi halin dai, an sako yaran su 344 wanda daya daga cikinsu ya tabbatar iyakansu ke nan, babu wanda ya rage ko ya rasu a hannun masu garkuwar.