Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi alkawarin fara daukar mataki a kan bankunan da ke boye sababbin takardun kudi suna bai wa ’yan siyasa.
CBN ya ce daga ranar Alhamis, zai fara bibiyar bankunan don gano wadanda a cikinsu ke kin bayar da sababbin tsabar kudin.
- Mutumin da ya yi wa uwa fyade a gaban ’yarta ya shiga hannu
- An tura ’yan kwaya 3,500 cibiyar gyaran hali a Afghanistan
Shugaban CBN din reshen jihar Kwara, Mista Benedict Maduagwu ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, yayin taron wayar da kai ga kananan ’yan kasuwa da ke kasuwar Onitsha a jihar Anambra.
“Daga yau, CBN zai fara daukar mataki kan bankunan da ke boye sabon kudi da gangan.
“Za mu fara bin su daya bayan daya don tabbatar da sun bai wa mutane, ba wai ’yan siyasa kadai ba,” in ji shi.
Ya kuma ce ba a sabunta takardun kudin don cuzguna wa ’yan Najeriya ba, sai don kare martabar kudin Najeriya da kuma kawo karshen boye tsabarsu da wasu ke yi a gidajensu da kuma kawar da wadanda suka tsufa.