Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zargi wasu bankuna da yi masa zangon kasa ta hanyar boye sabbin takardun kudade tare da ci gaba da bayar da tsofaffi.
Hakan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 10 a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a kasar nan.
Babban Jami’in bankin a Jihar Ribas, Maxwell Okafor, ne ya yi zargin a Fatakwal, babban birnin Jihar lokacin da ya jagoranci ayarin CBN yayin ziyarar duba yadda bankuna da kasuwannin Jihar ke ta’ammali da sabbin kudaden ranar Juma’a.
Ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a kawai, CBN ya ba bankunan kasuwancin da ke jihar tsabar kudin da suka kai Naira biliyan hudu da rabi, inda ya nuna damuwa kan yadda har yanzu jama’a ba sa samun su.
Ya ce, “Mun jima muna sanya idanu a kan yadda ake ba da sababbin kudade, kuma abin da muka gano ba ya karfafa mana gwiwa.
“Mun ziyarci wasu bankuna, kuma daya daga cikinsu har yanzu yana bayar da tsofaffin kudi. Wasu injinan ATM dinsu kuma ba sa aiki, kuma mun ji cewar ko kafin mu karaso nan, CBN ya ba su sabbin kudaden.
“Wasu daga cikin bankunan sun karbi sabbin kudaden, amma sun je sun boye su.
“CBN na gargadin cewa akwai tsattsauran mataki ga duk bankin da ke boye kudaden yana ba wasu shafaffu da mai.
“Mun daina bayar da tsofaffin kudade tun da sababbin suka fito, don haka ban ga dalilin da zai sa ATM ya ci gaba da bayar da su ba,” in ji Babban Jami’in.
Shi ma Daraktan Tsara Manufofi na bankin, Emenike Chimele, ya ce ko shakka babu wasu daga cikin bankunan na kokarin yi wa CBN zagon kasa kan sabuwar manufar.
Idan za a iya tunawa, CBN ya tsayar da 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a Najeriya.
Sai dai yayin da ya rage ’yan kwanaki kafin cikar wa’adin, har yanzu mutane ma kokawa kan karancin sabbin takardun, yayin da har yanzu bankunan da injinan ATM ke ci gaba da bayar da tsofaffin takardun.